✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Attajiri Bill Gates ya saki matarsa, Melinda

Bill da Melinda sun ce sun yanke shawarar datse igiyar auren nasu ne saboda hakan zai fi musu fa'ida.

Fitaccen attajirin nan dan kasar Amurka kuma wanda ya kirkiri kamfanin Microsoft,  Bill Gates, ya sanar da rabuwa da matarsa, Melinda.

Rabuwar tasu na zuwa ne bayan sun shafe shekaru 27 a matsayin ma’aurata.

A cikin wata sanarwa da Bill Gates ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, Bill da Melinda sun ce sun yanke shawarar datse igiyar auren nasu ne saboda hakan zai fi musu fa’ida.

Sanarwar ta ce, “A tsawon shekaru 27 din da muka shafe tare, mun haifi ’ya’ya uku sannan mun assasa wata gagarumar gidauniya da take aiki a fadin duniya wajen inganta lafiya da rayuwar jama’a.

“Har yanzu tafiyarmu na nan a wannan fagen kuma za mu ci gaba da aiki tare a gidauniyar, amma ba a matsayin ma’aurata ba, saboda yanzu ra’ayoyinmu sun banbanta.

“Za mu dan yi nesa-nesa da juna yayin da kowa zai je ya gina sabuwar rayuwa,” inji sanarwar.

Tsoffin ma’auratan dai sun hadu ne a shekarun 1980, sannan suka yi aure a 1994, kuma suka haifi ’ya’ya uku –  Jennifer da Rory da kuma Phoebe.

Kazalika, sun kafa Gidauniyar Bill da Melinda Gates a shekarar 2000.

Bill Gates dai shine attajiri na hudu mafi kudi a duniya inda ya mallaki sama da Dalar Amurka biliyan 130

Ya kuma mallaki kaso 1.37 cikin 100 na kamfanin Microsoft, wanda darajarsa ta haura Dala biliyan 26.