✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Rukayya Dawayya ya mutu

A makon jiya ne auran tsohuwar shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da ‘Rukayya Dawayya’ ya mutu.Har zuwa lokacin hada…

A makon jiya ne auran tsohuwar shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da ‘Rukayya Dawayya’ ya mutu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san takamaiman abin da ya sanya auren ya mutu ba, amma wata majiya ta ce tsohuwar jarumar ta ce Allah ne Ya hada ta da wani irin miji wanda sakin mata a wurin sa ba komai ba ne. Domin akalla ya saki mata fiye da goma sha biyar, don haka idan ya sake ta ma ba zai zama wani abu ba.
Ta ce ba ta san tsohon mijinta nata da auri-saki ba, abin da ta sani shi ne matansa biyu da ’ya’ya 6, sai daga baya ta gano ’ya’yansa 11 kuma kowanne da mahaifiyarsa, sannan akwai wadanda suka fita ba su haihu ba.
Allah Ya albarkaci auren Dawayya da tsohon mijinta da da daya mai suna Umar Arfat, wanda aka haife shi a Makka a bara.
Idan ba a manta ba a ranar 6 ga watan Yuli, 2012 aka daura auren Rukayya Dawayya da dan kasuwa mazaunin Abuja mai suna Alhaji Muhammad Teku, bayan rasuwar tsohon saurayinta Mustapha Aliyu Tsanyawa, wanda dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Tsanyawa da kunci a Majalisar Dokokin Jihar Kano, watanni kadan kafin lokacin da aka sanya na bikinsu.
A yanzu dai an ce tsohon mijin Dawayya zai auri jaruma Fati Bararoji, sai dai har yanzu jarumar ba ta ce komai a kan batun ba.