✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Auren wuri na cikin manyan matsalolin ilimi a arewacin Najeriya’

Wani bincike da Gidauniyar Tallafawa Ilimi ta Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta gudanar ya gano cewa auren wuri na cikin manyan abubuwan da suka…

Wani bincike da Gidauniyar Tallafawa Ilimi ta Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta gudanar ya gano cewa auren wuri na cikin manyan abubuwan da suka jawo koma-bayan ilimi a arewacin Najeriya.

Binciken, wanda tsohuwar ministar ilimi Farfesa Rukayyatu Ahmad Rufa’ai ta jagoranta, ya kara da cewa talauci, karancin kayayyaki, rashin isassun malamai, da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ma na cikin manyan matsalolin.

Da take jawabi yayin gabatar da rahoton ranar Alhamis, Farfesa Rukayya ta ce binciken nasu ya mamaye kananan hukummi 419 na arewacin Najeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja.

COVID-19: Babu ranar sake bude makarantu —Minista

WAEC ta kama masu kula da jarabawarta suna magudi

“[Manyan matsalolin] da bincikenmu ya gano sun hada da rashin kudi a hannun iyaye da za su iya daukar nauyin ’ya’yansu – yawancin shirye-shiryen gwamnati na bunkasa ilimi ba sa kaiwa ga galibin iyaye musamman shirin ciyar da yara ’yan makaranta – da kalubalen ilimin ’ya’ya mata da kuma shigar da tsarin ilimin boko cikin makarantun almajirai na tsangayu,” inji ta.

Sai dai kuma binciken ya gano cewa yankin ba ya fama da matsalar rashin kwararrun malamai saboda kashi 70 cikin 100 na malaman yankin sun cancanta kuma suna da akalla takardar shaidar karatu ta NCE zuwa sama, yayin da kashi 52 cikin 100 ke da shaidar ta NCE.

Abu na gaba

Farfesa Rukayya ta kuma ce rahoton nasu ya gano cewa ilimi ba ya samun hakikanin kulawar da ta dace a yankin, musamman a bangaren samar da kudade da kayayyakin da ake bukata, lamarin da a cewarta ya taimaka matuka wajen tabarbarewarsa.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya yaba wa binciken ya kuma yi kira da a raba wa dukkan gwamnonin yankin, yana mai bayar da tabbacin cewa za su yi nazari na tsanaki a kansa su kuma aiwatar da shawarwarin da ya kunsa.

Shi kuwa gwamnan Jihar Kaduna wanda kwamishinansa na ilimi, Shehu Usman Mohammed, ya wakilta, cewa ya yi jiharsa ta jima tana bayar da fifiko ga harkar ilimi inda ko a ’yan watannin nan ta dauki sabbin malamai tare da gyarawa da kuma gina azuzuwa da dama.