✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Yusuf Buhari da ’yar sarkin Bichi: Yadda mutane suka fara dafifi a Fadar Sarki

Za a daura auren ne a babban Masallacin Juma’ar garin bayan Sallar Juma’a.

Duk da tarin jami’an tsaron da aka jibge, mutanen garin Bichi da kke Jihar Kano, al’ummar garin sun fara yin dafifi zuwa Fadar Sarkin garin domin halartar daurin auren ’yar Sarkin garin.

Zahra, wacce daya ce daga cikin ’ya’yan Sarkin Bichin, Alhaji Nasiru Ado Bayero za ta amarce da angonta, Yusuf, da ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan da ’yan sa’o’i masu zuwa.

Za a daura auren ne a babban Masallacin Juma’ar garin bayan Sallar Juma’a.

Lokacin da wakilan Aminiya suka isa garin wanda ke da kimanin nisan kilomita 30 Arewa da birnin Kano, sun iske wasu mutane wadanda suka halarci wajen tun da misalin karfe 6:00 na safe saboda ba sa so a basu labari.

Kazalika, Aminiya ta lura cewa an jibge jami’an tsaro a garin, yayin da jami’an Hukumar Tsaro ta DSS suka yi wa masallacin kawanya ta kowacce kusurwa.

An kuma hangi jami’an ’yan sanda a sassa da dama na garin inda suke ci gaba da sintiri a daidai lokacin da manyan baki ke kara shiga garin.

A cikin birnin Kano kuwa, wakilan namu sun lura da yadda aka jibge jami’an tsaro a kusan dukkan manyan titunan garin.

Daya daga cikin manyan hanyoyin da suka fi tara cunkoson ababen hawa ita ce hanyar zuwa Katsina, wacce ita ce hanya daya tilo ta shiga garin na Bichi daga Kano.

Tawagar ta kunshi Ministan Tsaro, Bashir Magashi da na Aikin Gona da Raya Karkara, Sabo Nanono da na Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da kuma na Albarkatun Ruwa, Sulaiman Adamu dukkansu karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.