✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba biyan albashi aka zabe ni in yi ba —El-Rufai

Gwamnan Kaduna ya ce don ya samar da tsaro da sauransu aka zabe shi ba biyan albashi ba kawai

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba don  biyan albashin ma’aikata kawai aka zabe shi ba, sai domin ya kawo wa Jihar cigaba.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana game da sallamar ma’aikata 4,000 da gwamnatinsa ta yi a kananan hukumomi 23 na Jihar.

“An zabe ni domin in samrar da adalci, in kuma gina tare da gudanar da makarantu da asibitoci, in inganta abubuwan jin dadin rayuwa da kuma samar da tsaro ta yadda kamfanoni za su yi sha’awar zuwa su zuba jari tare da samar da ayyuka a Jihar,” inji sanarwar da kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Litinin.

El-Rufai ya ce yawan kudaden albashin ma’aikatan ya jefa gwamnatin jihar cikin matsi, uwa uba, kudaden da take samu daga Gwamnatin Tarayya ba su taka kara sun karya ba.

“A watan Nuwamban 2020, Naira miliyan 162.9 kacal ne ya rage wa Gwamnatin Jihar Kaduna daga cikin biliyan N4.83 da ta samu daga Gwamnatin Tarayya, bayan da ta biya albashin biliyan N4.66,” inji shi.

A cewarsa, tun daga wata shidan karshen 2020, da kadan kudaden da jihar take samu daga Gwamnatin Tarayya, ya dara abin da za ta biya kudaden albashi da gudanar da ma’aikatun gwamanti.

“A wata shidan, albashi ke cinye kashe 84.97% zuwa 96.63% na kudaden da Jihar Kaduna take samu daga Gwamnatin Tarayya. A watan Maris din 2021, miliyan N321 ne ya rage mata bayan ta biya albashi,” inji shi.