✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba cin bashi ba ne babbar matsalar Najeriya – Ministar Kudi

Ta ce karancin hanyoyin kudaden shiga ne ya kamata su dami jama'a ba cin bashin ba.

Duk da yadda Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar ciyo bashin sama da Naira tiriliyan shida don cike gibin kasafin kudin 2022, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce cin bashin ba shi ne babbar matsalar Najeriya ba.

Ta ce karancin wadatattun hanyoyin samar da kudaden shiga don aiwatar da manyan ayyuka da kuma al’amuran yau da kullum ne ya kamata su rika ci wa ’yan Najeriya tuwa a kwarya.

Ministar na wadannan kalaman ne yayin da take yin fashin baki a kan kasafin kudin, inda take kare yunkurin gwamnatin na ciyo bashin.

A ranar Alhamis ne dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin da ya haura Naira tiriliyan 16, inda ya ce tiriliyan shida daga ciki bashi za a ciwo.

Sai dai Zainab ta ce adadin kudin na tiriliyan 16 sun yi kasa matuka in aka kwatanta da tiriliyan 100 na jimlar kudaden da ake juyawa a tattalin arzikin kasar.

Ta ce, “Matsalarmu ita ce kudaden shiga, kuma muna aiki ba dare ba rana wajen lalubo kudaden da zamu samar don tafiyar da gwamnati da kuma rage basussukan.

“Cin bashin yana da muhimmanci saboda mu sami damar aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.”

Ministar ta ce gwamnati na cin bashin ne don ta yi manyan ayyukan da zasu samar wa da ’yan kasa ayyukan yi, su kara yawan kudaden da suke yawo a hannun mutane sannan su bunkasa haraji.

Hajiya Zainab ta ce basukan da ake bin kasar sun yi tashin gwauron zabi ne saboda matsin tattalin arzikin da kasar ta fada har sau biyu a cikin ’yan shekarun nan.

Har ila yau, ta zargi kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta da cewa shi ne ya sa aka warewa bangaren tsaro kaso mafi tsoka na kaso 22 cikin 100 a kasafin na badi.