✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Ba za mu kara farashin kayan abinci ba –’Yan Kasuwar Singa

'Yan kasuwar sun ce ba su da hannu wajen kara farashin kayan abinci a jihar.

’Yan Kasuwar Singa a Jihar Kano, sun yi alkawarin rashin kara farashin kayan masarufi albarkacin watab Ramadan da ke tafe.

Kungiyar ’yan kasuwar ta kuma musanta zargin da ake musu na boye kayan abinci don sanya farashin kayan masarufi ya yi tsada.

’Yan kasuwar wadanda suka halarci ofishin Hukumar Karbar Koke-Koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar (PCACC), sun nesanta kansu da kara farashin kayayyaki.

Shugaban ’yan kasuwar, Ibrahim Danyaro ya ce: “Ba ma boye kayan abinci da sauran kayayyaki shi ya sa muka zo nan yau don tattauna matsalar da PCACC.

“Mun zo da takardun shaida kuma sun fahimci cewar ba mu da hannu a tashin kayayyaki, mu ‘yan kasuwa ne da ke sayen kaya daga kamfani, kuna muna sayarwa a mafi karancin farashi idan aka kwatanta da sauran kasuwanni.”

Aminiya ta ruwaito a ranar Lahadi hukumar ta kai samame tare da rufe wasu rumbunan ajiyar kayan abinci biyar a kasuwar Dawanau da ke jihar.

Kazalika, da yake mayar da martani wani dan kasuwa, Hamisu Rabiu, ya tabbatar wa ‘yan jarida a jihar cewar za su duk mai yiwuwa don ganin farashin kayayyaki bai tashi ba duba da karatowar watan azumi.

“Kamar yadda muka fada ba mu da hannu a tashin farashin kayayyaki, mu ma fama muke yi da lamarin. Amma za mu yi duk mai yiwuwa don hana tashin kayayyaki. Wannan alkawari ne musamman duba da karatowar azumi.

“Matsalar ba tamu ba ce amma mun fada wa hukumar ta zauna kamfanoni don jin inda matsalar ta ke daga wajensu.”

A nasa bangaren, Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce sun gamsu da jawabin ‘yan kasuwar amma duk da haka akwai bata gari a cikinsu, shi ya sa hukumar ta rufe wasu rumbuna.

Ya jaddada aniyar hukumar da gwamnatin jihar na saka kafar wando daya da ‘yan kasuwar da ke boye kayan abinci da nufi kara farashi.

“Mun gamsu ba sa yin hakan kuma sun nuna a shirye suke su taimaka wajen kawo karshen matsalar. Muna son sanar da jama’a duk ‘yan kasuwar da ba su da burin fito da kayansu suna boye su ne.

“Muna sane da wadanda suke boye kaya don kara farashi kuma muna nan zuwa gare su. Kuma muna rokon jama’a da su taimaka mana wajen yaki da wannan matsalar.”