✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu kai karar Shugaban INEC kotu ba —DSS

DSS na sane da yadda wasu miyagu ke son tayar da rikici a kasar nan.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta musanta labarin da ke yawo cewa tana cikin hukumomin tsaron da suka maka Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu a kotu.

Kakakin rundunar, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai, inda ya yi karin haske kan umarnin wata Babbar Kotun Abuja na hana hukumomin tsaro ciki har da DSS din kama Yakubu.

A ranar Laraba ce dai Alkalin Kotun, M. A. Hassan ya ki amincewa da bukatar tsige shugaban INEC din daga mukaminsa, saboda zargin kin bayyana ainihin kadarorin da ya mallaka.

Alkalin ya ce kadarorin da Yakubun ya bayyana haka suke, kuma sun yi daidai da tanadin dokokin Najeriya.

Hukuncin dai ya biyo bayan karar da Somadina Uzoabaka ta shigar da Babban Lauyan Gwamnatin da Farfesa Yakubu mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022, don tilasta wa shugaban hukumar ta INEC sauka daga matsayinsa, har sai an gudanar da binciken wasu zarge-zargen da hukumomin tsaro daban-daban ke yi masa.

Sai dai Afunanya ya ce kwata-kwata DSS ba ta cikin hukumomin tsaron da suka shigar da waccan karar.

“DSS na sane da yadda wasu miyagu ke son tayar da rikici a kasar nan, gami da haifar da cece-kuce game da babban zabe mai zuwa.

“Kuma wannan na daya daga cikin dabarun su na yin zagon kasa da lalata kokarinmu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

“Don haka ina amfani da wannan dama, don wanke DSS da kuma fahimtar da al’umma cewa, ba gaskiya ba ne cewa mun kai karar shugaban INEC kotu”, in ji Kakakin.