✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu zargi Buhari da gazawarmu ba — Shettima

Wannan shi ne lokaci mafi wahala na riƙe muƙami a Najeriya saboda ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnati mai ci ba za ta zargi gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da ƙalubalen da take fuskanta bayan hawanta mulki ba.

Da yake jawabi a wajen taron da kafar yaɗa labarai ta 21st Century Chronicle ta shirya, Mataimakin Shugaban Kasar ya ce wannan shi ne lokaci mafi wahala na riƙe muƙamin siyasa a Najeriya saboda ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya duƙufa wajen magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta ne maimakon yin shirin da baida fa’ida.

“Shugaban ƙasa ya ɗauki matakan da za su ceci rayukan jama’a a maimakon wadanda za su kara jefa jama’a cikin ƙunci da durƙushewar tattalin arzikin ƙasar.

“Ba za mu ɗora laifin a kan gwamnatin da ta gabata ba, domin shugabanci ya shafi jajircewa mai ɗorewa.”

“Kafin mu karɓi mulki, babban lamarin shi ne batun cire tallafin mai. Matsalar da ta ci gaba ta ci wa ’yan Nijeriya tuwo a ƙwarya tsawon shekaru 20 zuwa 30 da suka gabata.

“Mun fahimci dalilin da ya sa magabatanmu suka yanke shawarar cire tallafin don haka suka yi tanadin cire tallafin man fetur ɗin a cikin Kasafin Kuɗi.

“Shekara ɗaya kafin mu hau mulki, bashin Najeriya ya ƙaru da kashi 111.18. Wanda hakan kamar naƙasu ne ga tattalin arziki.

“Mataki ne na matsin tattalin arziki. Domin mu fahimci yadda lamarin yake, kamar a ce kana samun Naira 100,000, sai a tilasta maka ciyo ƙarin Naira 11,800 don biyan wanda ake bi bashi. Ta yaya za mu tsira a wannan yanayin? Za a daɗe kafin mu mu daina karɓa.”

Ya ƙara da cewa tallafin ya haifar da karkatar da albarkatun ƙasa zuwa ga sassa masu muhimmanci da kuma dakile cin hanci da rashawa da tsarin tallafin ya haifar.

“Dole ne mu yi watsi da tsarin tallafin man fetur, magani ne mai ɗaci wanda dole mu haɗiye amma dole ne mu yi.”