✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu abin da Ganduje zai tsinana wa Tinubu a 2027 — Kwankwaso

Tinubu zai yi nadamar kulla hulda da Ganduje saboda ’yan Najeriya sun dauke shi a matsayin mayaudari.

Jagoran jam’iyyar NNPP na Kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya caccaki babban abokin hamayyarsa na siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

A cewar Kwankwaso, Ganduje tamkar wani ƙarfen-ƙafa ne ga jam’iyyar APC mai mulki wanda ba zai tsinana wa Shugaban Kasa Bola Tinubu komai ba a Zaben 2027.

Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na NNPP Honarabul Yakubu Shendam ya fitar, ya yi martani kan kalaman da Ganduje ya yi a Larabar wannan mako da cewa “in dai rashin nasara ce a siyasa to kuwa Kwankwaso yanzu ma ya fara gani.”

Da yake karbar Haliru Jika da ilahirin shugabannin jam’iyyar NNPP a Bauchi, Ganduje ya ce “Lokacin da na samu labarin cewa za ka zo ganina don tattaunawa a kan hanya mai bullewa, na san na hadu da wani jigon dan siyasa, wanda kowa ya san shi a Bauchi.

“Ya dawo zuwa jam’iyyar masu ra’ayin ci gaba da kuma alkibla, musamman ganin inda ya baro. Ya taho daga wata jam’iyya wadda a baya ta kasance mai daraja da matukar kima, amma daga baya sai Kwankwasiyya ta karkatar da ita, ta gurbata ta.

“Muna farin cewa NNPP ta ainhi ta dawo kuma ta hau kan cikakken matsayinta, inda ta yasar da kungiyar Kwankwasiyya, duk ta yi watsi da ita gaba daya.

A martanin, Shendam ya bayyana cewa, la’akari da kashi-a-gindin da ya dabaibaye Shugaban APC na kasa, duk wani dan Najeriya da ya wadata da hankali ba zai dauki Gandujen da wani muhimmanci ba.

Ya kara da cewa, babu wata fa’ida da za a samu a tattare da Ganduje duba da irin mummunar badakalar da ake zarginsa da ita, wanda wannan dalili da ba zai iya tabuka wa Tinubu ko jam’iyyar APC komai a 2027.

“Ai kasancewar Ganduje shugaban APC, to kuwa jam’iyyar tamkar mushe take domin ta mutu murus ke nan.

“Ko a yarda ko kar a yarda, Ganduje koma-baya ne ga Tinubu da jam’iyyar APC da kuma kasa baki daya.

“Ba na tantamar cewa muddin Ganduje ne Shugaban APC, to kuwa Shugaba Tinubu ba zai yi nasara a Zaben 2027 ba, domin kuwa ’yan Najeriya ba za su zabe shi ba,” in ji Shendam.

Ya kara da cewa, “Tinubu zai yi nadamar kulla hulda da Ganduje saboda ’yan Najeriya sun dauke shi a matsayin mayaudari.

“Kar Ganduje ya manta cewa Sanata Kwankwaso ya zama gatansa a siyasa domin bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na gwamna, Kwankwaso ya dauke shi a matsayin abokin takararsa a shekarar 2003.

“Ya sake nada shi mashawarci na musamman a lokacin da ya zama Ministan Tsaro. Ya kuma ba sa aka ba shi shugabancin Hukumar Kula da Tafkin Chadi da ke Ndajemena, sannan ya sake daukarsa a matsayin mataimakin gwamna a 2011 zuwa 2015.

“Bayan Kwankwaso ya kammala waadin mulkinsa, ya zabi Ganduje a matsayin magajinsa a 2015, kuma daga baya ya ci amanarsa. Shi ya sa a yanzu babu yarda a tsakin duk wani gwamna da mataimakinsa.

Shendam ya kara da cewar, Ganduje bai taba samun nasara a zabe ba duk tsawon rayuwarsa, in ban da lokacin da ya shiga rigar Kwankwaso a shekarar 2015 ya samu kujerar Gwamna a bagar.

Duk wani dan Najeriya ya san labarin abin da ya faru a lokacin zaben Gwamnan Kano a 2019, wanda ba sai ana yi fashin-baki a kansa ba.

NNPP ta nanata cewa Kwankwaso wanda tsohon Gwamnan Kano ne, a tarihi ya yi takarar zabe sau 17 kuma a ciki ya yi nasara sau 14.

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ya kuma koka kan abin da ya bayyana a matsayin yunkurin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Ganduje na dakile muradun al’ummar Jihar Kano.

Ya yi gargadin cewa yunkurinsu na kwace Kano ta haramtacciyar hanya kamar yadda suka yi a 2019, nagartattun mutanen Kano da alkalai masu riko da shari’a ta gaskiya ba za su bari hakan ta sabu ba.