✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu bukatar shaidar gwajin COVID-19 daga wurin dalibai yayin komawa makaranta’

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta ce, babu wani sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ake da bukatar dalibai su gabatar da shi kafin su samu izinin…

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta ce, babu wani sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ake da bukatar dalibai su gabatar da shi kafin su samu izinin shiga makarantunsu.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimin, Mista Ben Goong ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da dalibai a fadin Najeriya ke komawa makarantunsu don ci gaba da karatu.

Goong, ya ce babu abunda ake da bukata ko gwadawa face fitar da sakamakon yanayin lafiyar dalibai ko na masu shiga makarantun tun daga bakin kofar shiga makaranta.

“Babu wata shaidar sakamakon gwajin cutar COVID-19 da hukumar gudanarwar makaranta za ta bukata a wurin dalibai da iyayen yara kafin su samu damar shiga makaranta,” in ji shi.