✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu dalibar firamare da aka lalata a Kano —Kwamishina

An ja hankalin al’ummaa cewa a duk inda aka samu faruwar wasu al’amura a riƙa sanar da gwamnati maimakon yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta bidiyon nan da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ke iƙirarin cewa an sami wata yarinya ’yar makarantar firamare da aka lalata.

Kwamishinan Ilimi  na jihar, Dokta Umar Haruna Doguwa  ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

A kwanakin baya ne tsohuwar jarumar Kannywood Mansurah Isah ta wallafa wani bidiyo a shafinta inda take kokawa bisa yadda wasu bata-garin yara suka lalata wata karamar yarinya da suke makarantar firamare tare.

A cewar Doguwa, sun samu Mansurah Isah kuma ta nuna nadamarta a kan abin da ta aikata wanda babu gaskiya a cikinsa inda ta bayar da tabbacin za ta goge wannan bidiyon.

“Duk da cewar ba a yin bari a kwashe tas. Amma mun same ta ta kuma nuna nadamarta kan abin da ta yi inda ta nuna cewa za ta goge bidiyon da ta wallafa wanda da a ce ta yi bincike sosai da ba ta wallafa shi ba”.

Doguwa ya ja hankalin al’umma cewa a duk inda aka samu faruwar wasu al’amura a riƙa sanar da gwamnati maimakon yaɗawa a kafofin sada zumunta.

“Ya kamata mutane su fahimci cewa yayin da suka ji irin wannan kamata ya yi su binciki gaskiyar lamarin kafin yada irin waɗannan abubuwa.

“Ba mu son yadda mutane suke yaɗa abubuwan da a haƙiƙanin gaskiya ba su faru a wata makaranta daga cikin makarantunmu ba.”

Kwamishinan ya gode wa ’yan jarida da Hukumar Hisbah ta jihar da Ma’aikatar lafiya da Hukumar Ilimin Firamare ta jihar (SUBEB) bisa gudummawar da suka bayar wajen warware lamurra cikin sauki inda ya yi fatan hakan ba zai sake faruwa a nan gaba ba.