Daily Trust Aminiya - Babu gwamnatin da ta fi ta Buhari yin ayyuka – Shehu Sani
Dailytrust TV

Babu gwamnatin da ta fi ta Buhari yin ayyuka – Shehu Sani

Tsohon Shugaban Kwamitin Kula da Basuka na Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani, ya ce tun da Najeriya ta koma tsarin mulkin dimokuradiyya a 1999, babu Shugaban Kasar da ya yi manyan ayyuka na zahiri kamar Buhari.

Sai dai ya zargi Gwamnatin Buharin da ciwo bashin da magadanta za su yi jibin goshi kafin su biya. Ta kuma yi gum da bakinta kan sharuddan biyan bashin wanda za a rika biya da arzikin Najeriya.