✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu sassauci ga masu taimakon Nnamdi Kanu

Gwamnati ta samo muhimman bayanai kan masu taimakon shugaban IPOB.

Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta raga wa duk masu taimaka wa shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ke hannunta ba.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ce binciken da ya kai ga kamo Kanu daga kasar waje ya bankado muhimman abubuwa sosai.

“Zuwa yanzu, binciken ya bankado abubuwa masu tarin yawa kan shugaban haramtacciyar kungiyar da masu taimakon sa,” inji ministan.

Ya ba da tabbaci cewa gwamnati na kara bincike kuma komai matsayin mutum a cikin masu taimaka wa Kanu, sai an hukunta shi kan cin amanar kasa, saboda “Duk matsayin mutum, bai fi kasar ba”.

“Sama da shekara biyu hukumomin tsaron kasar nan ke bibiyar shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB da ke yawo a gidaje da otal-otal da jiragen alfarma a kasashe daban-daban, tare da yin shiga na kasaita.

Ya bayyana mamakin yadda har wasu suka fara kira da a yi wa Kanu adalci, sai ka ce a baya ba a yi masa adalci ba, har aka ba da belin sa, amma ya tsere.

A cewarsa, “Kanu zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya ja wa mutanen da rikici ya ritsa da su a sakamakon tunzura tayar da rikici da ya yi ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da kuma Twitter.”

Game da ainihin inda aka cafke Kanu, ministan ya ce, “Abin da kawai zan ce shi ne an kama shi ne ta hanyar hazaka da jajircewar hukumomin tsaron kasar nan tare da hadin gwiwar kasashen da muke da kawance da su. kuma za mu ci gaba da mutunta dangantakar da ke tsakaninmu da su.”