✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakala: Tinubu ya sa a binciki ministar Jin-kai, Betta Edu

An bukaci shugaba Tinubu ya dakatar da ministar don gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan badakalar Naira miliyan 585.189 da ake zargin ministar jin-kai, Beta Edu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kungiyoyi da sauran jama’a suka rika matsa wa Tinubu lamba kan a gudanar da bincike a kuma hukunta ministar matukar aka same ta da laifi.

Kungiyoyin sun bukaci Tinubu ya sauke Betta Edu daga mukaminta don samun damar gudanar da ingantaccen bincike ba tare da samun wani katsalandan ba.

Tun da farko an zargi Betta Edu ne da rubuta wa Akanta-Janar na Tarayya wata wasika da ke bukatar ta sanya wadannan kudade a cikin asusun wata mata da ba a san kowace ce ba, lamarin da ya tayar da kura.

Sai dai jim kadan bayan fitar labarin, Akanta-Janar din ta ce ba ta saki wadannan kudaden ba, saboda doka sam ba ta ba ta damar sanya kudade a asusun wani mutum ba.

Kawo yanzu dai ofishin ministar ya ce ta umarci a biya wadannan kudade ne don bai wa marasa galihu a Jihohin Akwa Ibom, Legas, Kuros Ribas da Ogun a matsayin tallafi.