✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakanike ya shiga hannu kan neman sayar da motar da aka ba shi gyara

Bakaniken ya yi kokarin sayar da motar da aka ba shi gyara.

An kama wani bakanike mai shekara 25 yana kokarin sayar da motar wani mutum da ya ba shi gyara.

Kakakin ’yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce bayan karbar motar daga hannun mai ita don gyara, sai bakaniken ya nufi kasuwa zai sayar.

A cewar Hundeyin, bayan samun sahihan bayanai an kama bakaniken da wata mota kirar Toyota Camry mara lamba.

Hundeyin ya kara da cewa wanda ake zargin zai fuskanci shari’a da zarar an kammala bincike a kansa.

Ya shawarci masu motoci da su yi taka-tsan-tsan wajen bayar da motocinsu ga amintattun bakanikai.