✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakuwar cuta ta kashe mutum 17 a Benuwe

Akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon barkewar wata bakuwar cuta a karamar hukumar Okpeilo-Ogbadibo dake jihar Benuwe. Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa…

Akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon barkewar wata bakuwar cuta a karamar hukumar Okpeilo-Ogbadibo dake jihar Benuwe.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sakataren hukumar lafiyar jihar Sir Andrew Amee ya fitar a madadin Kwamishinan lafiyar jihar a ranar Talata.

“Mun samu rahoton bullar wata cuta da bamu gano kanta ba a karamar hukumar Okpeilo-Ogbadibo”.

“A ranar 9 ga watan Nuwamba mun samu rahoton mutuwar mutane 17 a sakamakon harbuwa da suka yi da cutar”.

“Yanzu haka muna da wanda ya kamu da cutar a asibitin koyarwa na jami’ar Benuwe inda ake kula da shi, ragowar kuma suna asibitoci daban-daban na jihar nan”, inji Amee.

Ya kara da cewa alamomin cutar sun hada da zazzabi, kasala, amai, gudawa, ciwon jiki da sauransu.

Har wa yau, Amee ya kara da cewa gwamnan jihar Samuel Ortom ya ware kudi ga hukumar lafiya ta jihar, domin gudanar da bincike tare da gano musabbabin bullar cutar.

Sannan ya ja hankalin jama’ar jihar da su kasance masu tsaftace muhallinsu domin guje wa kamu wa da cututtuka barkatai.