✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Balarabe ya zama shugaban Hukumar Gasar Tseren Mota ta Duniya

Shi ne mutum na farko da ba dan nahiyar Turai ba da zai jagoranci Hukumar

Tsohon dan wasan tseren mota, Mohammed Ben Sulayem, ya zama Shugaban Hukumar Tseren Mota ta Duniya (FIA).

A jawabinsa, ya ce, “Na gode wannan karamci da aka zabe ni a matsayin Shugaban FIA, kuma zan yi duk abin da ya dace domin kare martaba da hakkokin mambobi.”

Mohammed Ben Sulayem shi ne mutum na farko da ba dan nahiyar Turai ba da zai jagoranci Hukumar.

Zai jagoranci FIA ne bayan shugabanta mai ce Jean Todt, ya yi ritaya a ranar Juma’a bayan shafe shekara 12.

Mai shekara 60 dan asalin Hadaddiyar Daular Labawa, Mohammed ya samu kashi 61.62 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Abokin karawarsa kuma, Graham Stoker, dan kasar Birtaniya, ya samu kashi 36.62 na kuri’un da aka jefa.