✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Ballewar gada ta yi kisa a Bauchi

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon ballewar gadar da ta hada hanyar Bauchi-Ningi-Kano da ke kauyen Tsangaya, Karamar Hukumar Ningi, Jihar…

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon ballewar gadar da ta hada hanyar Bauchi-Ningi-Kano da ke kauyen Tsangaya, Karamar Hukumar Ningi, Jihar Bauchi.

Sun kama ce mutum daya ya jikata sakamakon ruwan gulbin da ya tafi da shi tare da mamacin.

Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana wa wakilin Aminiya ta wayar tarho cewa, “An yi kokari an ceto su bayan ruwan ya tafi da su, amma mutum daya ya mutu cikin gulbin daya kuma ya samu raunuka, an kuma kai shi asibiti “.

Wani mazaunin kauyen Tsangaya, Mohammed Kabiru ya ce ambaliyar ruwa ta haddasa barkewar gadar a daren Lahadi bayan ruwan sama da aka yi.

Ya ce ruwan ya kuma mamaye gonaki inda aka yi asarar amfanin gona mai dimbin yawa.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Suleiman, a lokacin ziyarar gani da ido ya ce gadar mahada ce ta garuruwa da dama na Arewa maso Yammacin jihar.

Suleiman da ya samu rakiyar Babban Sakataren Ma’aikar Ayyukan jihar da ma’aikatan gyaran hanya na Gwamnatin Tarayya (FERMA), ya jajanta wa al’ummar kauyen da masu ababen hawa da bala’in ya auka musu.

Ya kuma ce gwamnan Jihar, Bala Mohammad ya ce a gaugauta gyara gadar.

“Duk da cewar hanyar gwamnatin tarayya ce, Gwamnan ya ce kamfanin gina hanya na Triacta Nigeria Limited ya cigaba da gyaran gadar.

“Na yi magana da shugaban kamfanin, ya ce za su fara aikin da yamma ko gobe da safe in Allah Ya kaimu,” inji Kakakin Majalisar.