✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin CBN ya kama da gobara a Binuwai

Gobara ta tashin a Bankin CBN reshen Jihar Binuwai ranai Alhamis.

An samu tashin gobara a Babban Bankin Najeriya (CBN) reshen Jihar Binuwai a ranar Alhamis.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 7 na safe, kafin a samu kashe ta tare da taimakon jami’an kwana-kwana.

Wata majiya daga bankin ta ce ana zargin matsalar lantarki ce ta haddasa gobarar wadda aka yi sa’a ba ta kai ga kama sauran sassan ginin ba.

Da aka nemi jin ta bakinsa game da lamarin, Daraktan Hukumar Kwana-kwana na Binuwai, Injiniya Donald Ikyaaza, ya tabbatar da aukuwar hakan.

Ya kara da cewa, bayan da labarin gobarar ya isa gare su ne jami’ansu suka yi dirar mikiya a wurin kana suka kashe gobarar murus.

“Hakika, gobarar wadda ta faro daga ma’ajiyar mai na bankin ta yi karfi, sai dai jami’aina ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kashe ta,” in ji Ikyaaza.

Ya zuwa hada wannan rahoto, an ga jama’ar yankin sun ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.