✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barawon abinci ya kashe manomi a Zariya

Babu dama a kwabi matasan yankin sai su yi barazanar kashe mutum.

’Yan Bijilanti a kauyen Saye da ke Karamar Hukumar Zariya sun kama wani da ake zargin barawon kayan amfanin gona da abincin dabbobi ne bayan ya sokawa wani manomi wuka har lahira. 

Bayanai na nuna cewa da misalin karfe 8:30 na daren ranar Laraba ne, mutumin ya haura gidan marigayin inda ya sossoka mishi wuka a ciki.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, barawon mai shekaru 35 ya yi wannan aika-aikar ce saboda kama shi da manomin ya yi har sau uku yana satar kayansa, har ta kai ga shari’a gaban Mai Unguwa.

Sai dai a wannan karon ya je satar amfanin gona da marigayin ya shuka a gefen gidansa, sai matar manomin ta hango shi ta yi masa ihu, har aka bi shi aka kama shi.

Bayanai na ce wannan lamari wanda bai yi wa barawon dadi ba ya sha alwashin ganin bayan manomin da kuma matarsa saboda ta tona shi.

Barawon ya sami sa’ar kutsawa gidan marigayin inda ya soka masa wuka a ciki har wuri biyu ya bar shi hanji waje kuma jina-jina ya fice ya kama gabansa.

Sai dai ko da matar marigayin ta ankarar da jama’a abin da ya faru da mijinta nan da nan aka mi shi zuwa asibiti daga nan kum.

Tuni da barawon wanda ya fada komar ’yan bijilanti ya amsa da bakinsa cewa lallai shi ne ya aikata wannan ta’asa kuma ba tare da bata lokaci ba suka mika shi hannun ’yan sandan yankin.

Sai dai kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ya ci tura sakamakon rashin daukar waya.

Al’ummar yankin sun bukaci muhukanta da su kawo dauki saboda saboda yadda suke fuskantar barazanar da wasu bata garin matasa ke yi musu na cewa za su kashe duk wanda ya ke kwabarsu.

Mazaunan sun alakanta barazanar da matasan ke yi a yankin da shaye-shayen miyagun kwayoyi.