✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daba sun cinna wa Babbar Kotu wuta a Ebonyi

Harin ya haifar da zullumi tare da tilasta wa hukumomin jihar fara yin taka-tsan-tsan.

Wasu bata-gari sun banka wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi wuta a ranar Litinin da dare.

Akalla jami’an tsaron da ke gadin kotun biyu ne suka jikkata a yayin harin da aka kai da misalin karfe daya na daren ranar inda aka kona wani sashe na ginin kotun.

Rahotanni sun ce bata-garin sun yi amfani da fetur ne wurin tayar da wutar wacce ta yi sanadiyyar konewar sassa da dama na kotun, ciki har da dakin adana bayanai da kuma ofishin jami’an tsaro.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci kotun da safiyar Talata, ya iske an girke motocin jami’an ’yan sanda guda uku a muhimman wurare na kotun.

Sai dai duk yunkurinsa na shiga cikin harabar kotun ya ci tura saboda jami’an tsaro sun ce Magatakardar kotun ya umarce su da kada su bar kowa ya shiga ciki.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Loveth Odah ta ce maharan sun yi cincirindo ne lokacin da suka zo sannan suka cinna wa kotun wuta.

Aminiya ta gano cewa harin ya jefa tsoro a zukatan mutane da dama tare da tilasta wa hukumomin jihar fara yin taka-tsan-tsan.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu rahoton asarar rai ko daya ba sakamakon harin.

A ’yan kwanakin nan, jihohin yankin Kudu maso Gabas da dama na fama da hare-hare, wadanda galibi ake zargin kungiyar ’yan a-waren Biyafara ta IPOB da kaiwa.