✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci: ’Yan sanda sun soma bincike kan rikicin da ya barke a Bauchi

Ana zargin wata mata da wallafa bidiyon batanci ga Annabi (SAW) a dandalin sada zumunta.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan rikicin da ya barke a Karamar Hukumar Warji kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW).

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Umar Mamman Sanda ne ya tabbatar da hakan yayin da yake bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin wanda ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama da kona gine-gine guda 13.

A nasa bayanin, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil ya ce, “A ranar 20 ga watan Mayu, 2022 wasu matasa sun fusata sun kona gidaje shida da shaguna bakwai, yayin da wasu mutane da dama suka samu raunuka sakamakon wani farmaki da suka kai kan wata mata ‘yar shekara 40 mai suna Rhoda Jatau.

“Matasan sun kai farmaki kan matar wadda ma’aikaciya ce a wata Cibiyar Lafiya ta Karamar Hukumar Warji, wadda suka yi zargin cewa ta wallafa wani sako na batanci ga fiyayyen halitta a dandalin sada zumunta.

Wakil ya ce “Tun daga nan rundunar ‘yan sanda ta tura dukkan kwararrun jami’an kwantar da tarzoma wadanda suka yi kokarin suka shawo kan lamarin.

“Yanzu haka dai an kwantar da hankulan jama’a kuma kura ta lafa a yankin, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da sintiri don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.”

Ya ce, “Kwamishanan ‘yan sanda CP Umar Mamman Sanda ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, domin an samu zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.

“Ya kuma ba jama’a tabbacin cewa ‘yan sanda sun shawo kan lamarin kuma za a rika sanar da jama’ar game da matakin bincike da ake kanyi daga lokaci zuwa lokaci.”

Wakil ya ce ’yan sanda na bukatar iyaye da su sanya ido sosai kan ayyukan yaransu a unguwanninsu musamman matasa, don haka ya bukaci malaman addini da shugabannin al’umma da dattawa baki daya da su rika magana da matasa a kodayaushe don kaucewa duk wani abu da zai iya fusata jama’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa matar da aka zarga da janyo wannan fitina mai suna Rhoda Jatau, ta sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa bayan samun labarin cewa ta yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a cikin wani faifan bidiyo da ta yada ta dandalin sada zumunta.

Matar wacce ta fito daga garin Billiri na Jihar Gombe, tana zaman aure ne a Karamar Hukumar Warji da ke cikin Jihar Bauchi.

Bayanai sun ce ana zargin ta da yin kalaman batanci a cikin wani hoton bindiyo na tsawon mintuna biyu a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne bayan da Musulmai sun dawo daga sallar Juma’a, inda nan da nan rigima ta kaure a tsakanin matasan Musulmai da na Kirista a garin.

Majiyar ta shaida mana cewar lokacin da matasan yankin suka samu labarin faruwar lamarin, cikin fushi suka nemi kai farmaki ga matar amma sai suka tarar ta gudu domin neman tsira.

Sakamakon faruwar wannan lamarin, wasu sun ji rauni, inda yanzu haka suna samun kulawar likitoci a Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare.

Kazalika, majiyar ta ce matasan Musulmai sun yi kokarin kona wani Coci a yankin don nuna fushinsu.

Kawo yanzu jami’an tsaro suna ta kai-komo domin tabbatar da an kiyaye doka da oda a garin na Warji da ke Jihar Bauchi