✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batar biliyan N30: Majalisa ta gayyaci Akpabio

Majalisar ta sa a kamo mata shugaban hulumar Neja Delta ya zo tare da Akpabio domin yin bayani kan batar dabon Naira biliyan 30.

Majalisar Wakilai ta gayyaci Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio da sabon Mukaddashin Shugaban hukumar bunkasa yankin (NDDC).

Kwamitin Majalisar kan yankin Neja Delta ya gayyace su ne domin amsa tambayoyi kan zargin batar dabon Naira biliya talatin ma’aikatar.

Mukaddashin Shugaban hukumar, Farfesa Kemwbradikumo Pondei ya fice daga zaman bincike da Kwamitin ya fara a ranar Alhamis, lamarin da ya sa Majalisar ta bayar da umarnin a kamo shi.

Kwamitin ya kuma ce umarci Akpbio da ya zo tare da mukaddashin Shugaban hukumar a zaman da za a yi ranar Litinin.

Ya kumaba da umarnin sanar da shugaban na NDDC ta kafafen yada labarai da ko ma wace irin hanya ce cewa majalisar ta bayar da izinin a kamo mata shi.

Idan ba a manta ba Shugaban Buhari ya yi tir da rashin kunyar da jami’an gwamnati ke yi ‘yan majalisar inda ya ce ba zai lamunci hakan ba.