Bauchi: Abin da ya ci Doma ba zai bar Awe ba | Aminiya

Bauchi: Abin da ya ci Doma ba zai bar Awe ba

Idan za mu iya tunawa Gwamnatin Jihar Bauchi da ta shude ba wani abu ya kawar da ita ba face karya da farfaganda. Don haka muna kira ga Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Bala Mohammed (Kauran Bauchi) ya mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan da jama’a suke bukata ya guji masu bambadanci da za su yi ta yi masa kirari don su samu abin sawa a baka. Kada ya yarda ya mayar da Abuja ta zama wurin zamansa, ya zauna a jiha da mutanensa yana gudanar da ayyukansa kuma yana lura da abubuwan da ake gudanarwa. Akwai bukatar ya rika kai ziyarar ba-zata da ziyarar gani da idon a duk inda ya bayar da aiki.

Wani abin kuma shi ne Mai girma Gwamna Bala Mohammed, ya rika jan kunnen mukarrabansa tare da sanya idon kan yadda suke tafiyar da amanar da ya dora musu. Domin tun ba a je ko’ina ba mun fara jin yadda ake korafi da wadansu daga cikin wadanda ya nada kan yadda suka shigo da yunwa. Ayyukan da suka kamata su watsa a cikin jama’a, sai su kankane su ce su za su yi da kansu. Ma’ana akwai mutanen da ya nada a mukamai da suke yin kwangila da kansu maimakon bayar da ita ga wadansu ba tare da bin doka ba.

 

Alhaji Gambo Abdullahi Bababa

Shugaban Tsabtace Magungunan Gargajiya na Jihar Bauchi.07032096837.