Bauchi ta nada mai ba da shawara kan gwauraye | Aminiya

Bauchi ta nada mai ba da shawara kan gwauraye

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi

Gwamnatin Bauchi ta nada Balaraba Ibrahim a matsayin mai ba wa Gwamna Bala Mohammed shawara kan sha’anin mata marasa aure.

Nadin na Balaraba ya fara aiki ne nan take kamar yadda Sakataren Gwamnatin Jihar, Sabiu Baba ya sanar a cikin wasikar ta ranar Alhamsi.

Ya ce an ba ta mukamin ne “bisa la’akari da kwarewarta da kuma jajircewa da kyawanwan dabi’u na rikon amana”.

Ya kuma bukace ta ta yi amfani da sabon mukamin nata wajen ganin mata marasa aure sun ci moriyar kokarin gwamnatin jihar na samar wa jama’a romon demokradiyya.

“Ina taya ki murna murna tare da rokon Allah Ya taya ki riko a sabon mukaminki”, inji takardar nadin.