✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bene mai hawa 7 ya danne mutane a Legas

Ana kyautata zaton ginin ya danne mutum shida

Wani bene mai hawa bakwai da ake aikin gina shi a kan titin Oba Idowu Oniru a jihar Legas ya rushe tare da danne mutum shida a cikinsa.

Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar ta Legas, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ne ya tabbatar da hakan da sanyin safiyar Lahadi.

Ya ce tuni jami’ai suka fara aikin ceto da nufin zakulo mutanen da ginin ya danne.

Babban Sakataren ya kuma ce, “bayan zuwan jami’anmu wajen, wanda wani gini ne mai hawa bakwai da ake kan gina shi, sun tarar ya rushe.

“Ba a sami jin rauni ba, amma rahotanni sun tabbatar akwai mutum shida da ginin ya danne.

“Dole za a bukaci yin amfani da babbar motar hukumar wajen ceto mutanen da ginin ya danne. Tuni muka aike da jami’anmu, kuma aiki na ci gaba da wakana yanzu haka,” inji shi.

Jihar Legas dai ta sha fama da matsalar rushewar gine-gine, musamman a ’yan shekarun nan. Lamarin dai na jawo asarar rayuka da ta dukiya da kuma jikkata.

Ko a farkon watan Nuwamban bara dai sai da wani bene mai hawa 21 ya rushe, inda kusan mutum 40 suka mutu a sanadin haka, ciki har da mamallakin ginin.

A jihar ta Legas dai, gwamnatin jihar ta yi dokar da ta halasta mata kwace mallakar duk wani fili da gininsa ya rushe.