✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon batsa: Ministan Tsaro da Sakataren Gwamnatin Chadi sun ajiye aiki

Sun sanar da ajiye ayyukan nasu ne ranar Laraba

Ministan Tsaron Chadi, Daoud Ibrahim da Sakataren Gwamnatin Kasar, Haliki Choua Mahamat, sun ajiye ayyukansu bayan fitar wasu bidiyoyinsu na batsal guda biyu.

Rahotanni sun ce jami’an gwamnatin sun ajiye aikin nasu ne a ranar Laraba, bayan bidiyoyin nasu sun karade gari musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Kakakin Firaministan kasar, Saleh Kebzabo ne ya ce gwamnatin ta amince da ajiye aikin nasu, kodayake sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba.

Bidiyoyin dai da aka yada a ranakun Lahadi da Litinin, sun nuna mukarraban gwamnatin suna mu’amala da wasu.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai iya tabbatar da sahihancin bidiyoyin ko jin ta bakin tsofaffin jami’an gwamnatin domin su mayar da martani a kai ba.

Ba kasafai dai ake samun badakalar fitar bidiyoyin batsa ba a Chadi, wacce galibin ’yan kasar Musulmai ne.

(NAN)