✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon fallasa: Yau Jaafar Jaafar zai bayyana gaban majalisar Kano

Mawallafin jaridar Daily Nigerian da ke fitowa a Intanet, Jaafar Jaafar ya amince da ya bayyana yau Alhamis gaban majalisar dokokin jihar Kano. Majalisar dai…

Mawallafin jaridar Daily Nigerian da ke fitowa a Intanet, Jaafar Jaafar ya amince da ya bayyana yau Alhamis gaban majalisar dokokin jihar Kano.

Majalisar dai ta kafa kwamitin ne don tantance gaskiyar bidiyon da mawallafin ya saki da ke zargin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hanci da rashawa da aka yi zargin sun kai Dala miliyan 5 (kimanin Naira miliyan 1,800) ne don ganin an magance cin hanci da rashawa da ake fama shi a kasar nan.

Ana dai zargin Gwamnan ya karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila.

Jaafar Jaafar ya tabbar wa majalisar zai halarci zauren majalisar da misalin karfe 11 na safe.