✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Binciken Magu: Shin shugaban EFCC zai kai bantensa?

Kallo ya koma sama a Najeriya inda binciken shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, kan kudaden gwamnatin da aka…

Kallo ya koma sama a Najeriya inda binciken shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, kan kudaden gwamnatin da aka kwato ke ci gaba da daukar hankali.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san inda Magu yake ba, haka ma batun makomarsa a kan kujerarsa, wanda wasu rahotanni ke cewa an dakatar da shi daga kai.

Tun ranar Litinin ake ta rade-radin cewa hukumar tsaro ta DSS ta tsare shi, amma hukuomi su karyata, tare da bayanin cewa yana amsa tambayoyi ne a gaban kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa kan kudaden gwamnati da aka kwato.

Shin Magu zai fito salim-alim, ko kuma zai bi sahun sauran shugabannin EFCC wadanda dukkansu cece-ku-ce irin wannan ne ya yi karshen zamansu a hukumar?

Kwamitin binciken da tsohon Shugaban Kotun Koli, Ayo Salami ke jagoranta na tuhumar Magu da saba dokokin aiwatar da aikin EFCC.

Yana kuma fuskantar zargi 22 da suka hadar da na karkatar da wasu kudade da aka kwato daga hannun masu laifi.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin domin a ba wanda ake zargin damar kare kansa bisa takardar zargi da Ministan Sharia, Abubakar Malami, da DSS suka gabatar masa.

Sai dai kakakin ministan, Umar Gwandu ya ce ba shi da masaniya a kan wata takardar zargi da maigidansa ya rubuta ko kuma kama Ibrahim Magu da aka yi.

“Yanzu na ji maganar a bakinku, ni ba ni da masaniya kan haka”, inji Gwandu, a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi a ranar Litinin.

Zargin da Magu ke fuskanta

Daga cikin zarge-zargen da ake wa Magu akwai:

  1. Rashin bayar da gamsashen lissafin kudaden da EFCC ta kwato a hannun barayin gwamnati.
  2. Rashin yin biyayya ga ofishin Ministan Shari’a.
  3. Kin gabatar da kwararan hujjoji da za su taimaka wajen dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya.
  4. Sakaci da binciken kamfanin P&ID wanda ya haifar da rikicin da gwammnati ta shiga a gaban kotu.
  5. Rashin bin umarnin kotu na bude asusun wani tsohon darektan banki na kimanin N7 biliyan.
  6. Tafiyar wahainiya wajen daukar mataki kan jiragen ruwa biyu da Rundunar Sojin ruwa ta kwace.
  7. Fifita wasu jami’an hukumar EFCC a kan wasu.
  8. Kai wasu alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Ministan Shari’a ba.
  9. Sayar da dukiyoyin sata ga ‘yan uwa da abokan arziki da kuma abokan aikinsa.

Shin zai iya tsallake siradi?

Wata majiya ta ce kwamitin na Salami ya taba bincikar Magu a lokacin da Shugaba Buhari ya nada shi Shugaban rikon EFCC a shekarar 2015.

“Ina da tabbacin an sa Salami ya jagoranci wannan zaman ne don an san ba zai yi abin da ya dace ba”.

“Wannan ba karamin cibaya ba ne a yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati take yi, saboda a yanzu, Magu ba shi da mataimaki.

“Kwanan nan za ka ji an ce ya sauka daga kujerar a ba wani domin su aiwatar da bincike. Ban tsammanin Magu zai tsallake tsigewa ba a wannan lokacin”, inji ta, tun a safiyar Talata kafin a fara rade-radin dakatar da Magu.

Zargin mai karfi ne sosai

Haka kuma wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana wa Aminiya cewa da kyar aka gamsar da Shugaba Buhari ya aminta da a binciki Magu saboda takardar zargin da aka gabatar masa mai karfi ce.

“Magu shi ne sarkin yakin Buhari a yaki da cin hanci da rashawa, amma zargin na da karfi matuka da kawar da kai daga garesushi zai shafi mutuncin Buhari da mulkinsa.

“Ina mai tabbatar maka sai da Buhari ya yi ta maza kafin ya aminta a binciki Magu”, inji ta.

Yadda Magu ya kwana a hannun ‘yan sanda

Bayan karyatawar da kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya yi na cewar sun kama Magu, ‘yan sanda sun yi awon gaba da shi inda ya kwana a hannunsu.

An tabbatar cewar da misalin 10:15 na dare bayan kwamitin ya kammala yi masa tambayoyi, jami’an ‘yan sandan suka tafi da shi.

Kafin su tafi da shi, sai da aka dakatar da masu ba shi tsaro kafin aka shigar da shi cikin wata mota.

Wata majiya ta ce, da farko Magu ya ce a baya zai zauna amma suka bukace shi ya shiga cikin motar ya zauna kafin su tafi da shi ofishin binciken hukumar ‘yan sanda (FCID).

Haka nan kuma an ce ya so ya yi bore a kan tayin kwana cikin ofis, inda ya bukaci a saka shi cikin dakin masu laifi amma suka rallashe shi.

Shin zai tsallaka da kujerarsa?

Wasu na ganin binciken Magu na daga manyan alamun yunkurin da ake yi na tumbuke shi daga kujerarsa.

A wani kaulin kuma, an rawaito cewar tuni Fadar Shugaban kasa ta fara neman wanda zai maye gurbinsa.

Binciken makircin makiya ne

Shugaban Kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara almundahana Farfesa Femi Adekunle ya danganta binciken da abin da ya kira makircin masu ruwa da tsaki  ne a tafiyar wannan gwamnati.

Ya kuma alakanta shi da yinkurin sake hana Magun rike kujerarsa wanda a baya DSS da Majalissar Tarayya suka nemi su hana a ba shi a shekarun baya.

Buhari zai yi kasassaba ke nan?

“Idan ban manta ba, Malami ya taba bukatar Magu ya ba shi wani fayil mai dauke da wani babban laifi amma Magu ya hana.” Inji Adekule.

Saboda haka ya shawarci  Buhari da ya kalli abun da idon basira kar ya daba wa kansa wuka a yinkurinsa na yaki da cin hanci da rashawa.

“Kar ka manta, Magu shi ne jagora a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa.

“Amma a binciken da muka gudanar, har yanzu ba mu ga wani kokari da Malami yake yi ba na dakile cin hanci da rashawa”, a cewarsa.

Magu ya koma gefe a yi bincike —PDP

A nata bangaren, jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaba Buhari ya nuna zummarsa ta yaki da almundahana ta hanyar gaggauta umartar Magu ya sauka daga kujerarsa domin a samu damar gudanar da cikakken bincike.

Sanarwa da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce zargin da Ministan Shari’a ya yi a kan EFCC ya cancanci Buhari ya bari gaskiya ta yi halinta.

Ologbondiyan ya ce a tabbatar an sauke Magu daga kujerarsa domin a hana shi yin da wasu abubuwa da ka iya zama hana shaida na ganin an kama shi da laifi.

Yadda aka yi awon gaba da Magu

A ranar Litinin ne jami’an DSS suka tare shugaban na EFCC a hanyarsa ta zuwa taro a hedikwatar ‘yan sanda, suka kuma tusa keyarsa zuwa Fadar Shugaban Kasa inda ya fuskanci kwamitin Mai Shari’a Salami.

DSS ta karyata cewa kama shi ta yi, amma kuma bayan jami’anta sun mika masa takaddar gayyatar, ya nemi shiga ofishin amma suka hana.

Kwamitin binciken ya ci gaba da yi wa Magu Tambayoyi a ranar Talata, inda wasu rahotanni ke cewa har an dakatar da shi.

To, ko Magu zai tsallake wannan dambarwa? Idan kuma har guguwar da tafi da shi, mece ce makomarsa?