Biranen Amurka 2 sun fara buga takardar kada kuri’a da Larabci | Aminiya

Biranen Amurka 2 sun fara buga takardar kada kuri’a da Larabci

Takardar kada kuri’a da harshen Larabci.   Hoto: Aljazeera
Takardar kada kuri’a da harshen Larabci. Hoto: Aljazeera
    Rahima Shehu Dokaji

A karon farko a tarihin Amurka, mazauna jihar Detroit sun sami damar yin zabe da takardar kada kuri’a ta Larabci saboda Larabawa mazauna jihar.

Matakin dai na nuna yiwuwar samun karin yawan fitowar masu zabe da kuma ‘yan siyasa daga yankin Larabawa mazauna kasar.

An sanya akwatinan  zaben ne a zaben jihar ranar Talata, a biranen Dearborn da Hamtramck, da ke yankin Kudu maso Gabashin Michigan da ke kusa da Detroit, wacce matsuguni ce ga Larabawa masu yawa .

Shugaban gundumar Dearborn, Abdullah Hammoud, wanda shi ne ya jagoranci samar da takardun zaben, a tattaunawarsa da gidan talabijin na Aljazeera ya ce: “A cikin al’ummar da ka san cewa kusan kashi 50 na su na magana da harshe biyu, musamman Larabci, me yasa ba za a ba da dama ga wadanda ke son shiga ba da gudummawa cikin dimokuradiyya ba?

A wani zabe a shekarar 2004 a Michigan, jam’iyyar Democrat ta ba da takardun kada kuri’a na Larabci. Haka kuma a ranar Talata ma an sanya su a duka zabukan da gwamnati ta shirya.

A takardun Kuri’un dai bayar da bayanin jinsi da kuma gurbin shawarwari duk a cikin harshen Larabci aka buga, amma sunayen ‘yan takara da Turanci aka rubuta.

Majalisar kasar dai ta yi gyaran fuska ga Dokar Hakkin Zabe ta Amurka ta shekarar 1975 sakamakon bukatar hukumomin gwamnati na kasar na shirya zabe a yankunan da ke da dimbin mutanen da da ke da harshen uwa bayan turanci, don kara yawan akwatinan zaben ga masu magana da tsirarun harsuna  a kasar.

To sai dai dokar ba ta hada da Larabawa ba a ciki, sai a yanzu ne aka fara samu.