✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta hana matafiya daga Najeriya shiga kasarta

Dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Litinin 6 ga Disamba, 2021

Kasar Birtaniya ta haramta wa matafiya daga Najeriya shiga kasarta saboda bullar kwayar cutar COVID-19 samfurin Omicron.

Hukumomin kasar sun sanya sunan Najeriya a cikin jerin kasashen da hana bakinsu shiga kasarta ne a ranar Asabar.

Sanarwar da Gwamnatin Birtaniya ta fitar ta ce, “Za a sanya Najeriya a cikin jerin kasashen daga karfe 4 na asuba ranar Litinin 6 ga Disamba saboda bullar kwayar cutar Omciron da aka samu a kasar da kuma mutum 134 da suka harbu da ita a fadin kasar Birtaniya.

“Daga ranar 7 ga wata kuma duk wani dan shekara 12 zuwa sama da ke son zuwa Birtaniya sai ya gabatar da shaidar gwajin (LFD ko PCR) da aka yi masa awa 48 kafin tafiyar domin dakile yaduwar kwayar cutar.”

A makon nan ne da dai Hukumar Yaki da Cututttuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tabbatar da harbuwar mutum uku da kwayar cutar Omicron a Najeriya.

Sanarwar da gwamnatin Birtaniya ta fitar ta ce hanin bai shafi matafiya da jiragen da wucewa kawai za su yi ta kasar ba.

Umarnin bai shafi matafiya ’yan kasar Birtaniya da mazauna da ’yan kasar Irelanda ne kadai za a bari su shigo kasar daga Najeriya.

Su ma din, “Wajibi ne a killace su na tsawon kwana 10 a cibiyoyin da gwamnati ta tanadar inda za a yi musu gwajin PCR sau biyu, a matsayi matakin dakile kwayar cutar.”

Sai dai ta ce matakin da ta dauka na wucin gadi ne a halin yanzu