✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Attahiru mai fada da cikawa ne —Zulum

A wata hudu Janar Attahiru ya je Borno sau shida don kara wa sojoji kaimi.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya nuna a aikace cewa zai yi duk mai yiwuwa wurin murkushe kungiyar Boko Haram.

Zulum ya ce daga nada Jannar Attahiru a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa a watan Janairu zuwa rasuwarsa a watan Mayu, ya tsaya kai da fata a yaki da kungiyar, inda sau shida yana zuwa Jihar Borno domin ganin sojoji da kama musu kwarin gwiwa a yaki da kungiyar.

“Jajircewarsa a yaki da Boko Haram a fili ta ce. Cikin dan lokacin da aka nada shi ya ziyarci Jihar Borno sau da dama, yana ganawa da kwamandoji da sojojin da ke bakin daga — a-kai-a-kai yana kara musu azama,” inji Zulum.

Ya ce tsayuwar dakar da marigayi Janar Attahiru ya yi domin kawo karshen ayyukan ta’addanci ta nuna a bayyana cewa shi mutum ne mai fada da cikawa.

Ya ce a lokacin ziyarar, Janar Attahiu kan bi sansanonin soji inda yake kara wa dakarun da ke bakin daga kaimi a aikin da suke yi na samar da tsaro da aminci.

Gwamnan Bornon ya bayyana haka ne ranar Asabar tare da magabacinsa, Sanata Kashim Shettima a wurin jana’izar marigayi Janar Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama a ranar Juma’a.

“Mutanen Borno na godiya a gareshi da sauran dakarun da suka kwanta dama a fagen fama bisa gudunmawarsu mara adadi ga Jihar Borno da kuma Najeriya baki daya,” inji shi.