✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Boko Haram ba Musulunci ba ne —Dar Al Andalus

Musulunci ya yi hannun riga da Boko Haram, amma ’yan ta’addar na yaudarar mutane da sunansa

Cibiyar Cigaban Zaman Lafiya da Koyarwar Addini ta Dar Al Andalus, da hadin gwiwar cibiyar ‘Corduba Peace Institute’, da ke Geneva sun horas dan ’yan jarida kan bambancin da ke tsakanin addinin Muslunci da akidar ta’addanci.

Taron da ya gudana a Yola, Jihar Adamawa ya tattauna kan hanyoyin guje wa akidar Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci, ganin yadda suke shigar rigar Musulunci.

Dokta Nurudden Lemo, ya bayyana wa taron cewa Musulunci ya yi hannun riga da ta’addanci, amma ’yan ta’adda suna amfani da sunansa wurin rinjayar mutane zuwa akidar tasu, wadda ba Musulunci ba ne.

A cewarsa, yadda wasu kungiyoyin ta’addanci ke saurin gushewa, wasu kuma kan dade, ne ta sa ake mujadala kan koyarwar kungiyar Boko Haram da wasu ke dangatawa da Musulunci.

Ya ce an gayyato ’yan jarida daga jihohin Arewa-maso-Gabas ne domin a ilimantar da su kan illolin kungiyoyin, saboda su ne idan suka fahimta, za su yaye wa al’umma duhun kai.

Shi ma Dokta Mansur Isah Yelwa, cewa ya yi a matsayin ’yan jarida na jigon samar da zaman lafiya a cikin al’umma, an fadakar da su ne ta yadda za su fahimtar al’umma yadda Musulunci ya yi hannun riga da akidun ta’addanci.

Ya ce karuwar kungiyoyin masu karkatar da mutane daga hanyar Allah zuwa bin son zuciya na bukatar masana labarai su ilmantu domin su wayar da kan al’umma ta hanyar labaransu.

Wani dan jarida da ba Musulmi ba ne da ya halarci taron, Williams Attah, ya ce ya ilimantu sosai da taron.

Ya ce a matsayin sa na wanda ba Musulmi ba, kafin taron ba ya iya bambance tsakanin da’awar Malaman Islama na hakika da na ’yan ta da kayar baya.

Ita ma Malama Bushira daga gidan Radiyo Fulaku FM Yola, ta ce a matsayin ta na ’yar jarida, yanzu ta samu ilimin yadda za ta kiyaye rahotannin malamai da na wasu masu da’awar da ba ta fahimci akidarsu ba.