✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram za ta yi musayar daliban Katsina da mayakanta

Kungiyar Boko Haram za ta nemi kudin fansa ko musayar daliban Makarantar Kankara da mambobinta da ke tsare a hannun Gwamnatin Najeriya, a cewar majiyoyinmu…

Kungiyar Boko Haram za ta nemi kudin fansa ko musayar daliban Makarantar Kankara da mambobinta da ke tsare a hannun Gwamnatin Najeriya, a cewar majiyoyinmu ranar Talata.

Kwararan majiyoyin sun fadi hakan ne bayan sakon sautin shugaban Boko Haram a safiyar Talata da ke ikirarin kungiyar ce ta yi garkuwa da daruruwan daliban GSSS Kankara, a ranar Juma’a da dare.

Ya ce dalibai 523 na hannunsu, yayin da Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce yara 333 ne, amma binciken Aminiya ya gano cewa dalibai 668 ne ba a gani ba. Daga baya a ranar Talata Gwaman ya ce an gano karin dalibai.

 

Shin Shekau ne ya yi magana?

Kwararru a fannin tsaro da kuma masu kusanci da kungiyar Boko Haram da muka tattauna da su sun tabbatar cewa mayakan bangaren Shekau na Boko Haram ne suka yi sace daliban.

Sai dai sun bayyana tantama game da ko Shekau ne ya yi magana a sakon muryar da kungiyar ta fitar.

Sun ja hankali da cewa a wannan karon mai jawabin ya kira kansa Abubakar Shekau kai tsayi, sabanin yadda ya saba kiran kansa, Abu Muhammad Asshakawi.

Daya daga cikin kwararrun ya bayyana tababarsa kan yadda mai jawabin ke inda-inda wurin karan sunan kungiyar: Jama’atu Ahlis-Sunnah Lidda’awati Wal Jihad.

Ya ce, “Amma in banda wadannan bambance-bambancen, a bayyane yake cewa sakon Boko Haram ne kuma ita ce ta dauke yaran.

 

Boko Haram a Arewa maso Yamma

“Mun dade muna cewa ayyukan ta’addanci sun yadu zuwa Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya…Yawancin tsiyatakun da ake yi, ana iya dangantawa da su, amma sakonsu na jiya ya tabbatar da komai,” inji tsohon hafsan sojin.

Bayan sojoji da hukumomin tara bayanai sun matsa wa kungiyar lamba a 2015 da 2017, sai ta takaita ayyukanta zuwa yankin Tabkin Chadi da Kudancin Jihar Borno, da kuma Yobe da Adamwa.

Sace daliban GSSS Kankara shi ne babban harin da kungiyar ta taba kaiwa a wajen yankin Tabkin Chadi da jihohin Borno, Yobe da Adamwa.

A sakon kungiyar, mai jawabin ya ce sun kai harin ne domin “yada Musulunci da kuma yakar kafirci.”

“Wannan aiki da ya faru a Katsina, don addini ya daukaka, kafirci ya yi kasa ne muka yi wannan aiki.

“Karatun boko ba karatun Allah da Annabi ba ne ba kuma abin Allah da Annabi ake koyarwa a ciki ba.

“Sai dai ma addinin Musulunci ne ake rusarwa a ciki”, inji shi.

 

Nan gaba Boko Haram za su gindaya sharuda

Kwararre a fannin tsaro, Salihu Bakhari ya shaida wa Aminiya cewa nan gaba kungiyar za ta sa wa gwamnati sharadi kan daliban na Kankara.

“Ba su da lokacin ajiye yaran su dade. Na gano cewa sun rarraba yaran ne sun ajiye su a yankunan Zamfara, Katsina da Kaduna a halin yanzu.

“Don haka wajibi ne Gwamnati ta yi maza ta dau mataki kar a maimaita irin abin da ya faru lokacin da aka sace daliban Chibok.

“Ina tabbatar maka cewa wurin da aka sace da dalibai ba irin wanda Boko Haram ke so ba ne…Ya yi nisa da Arewa maso Gabas, tafiya da yara masu yawa haka zai yi musu matukar wuya.

“Ina kyautata zaton nan ba da jimawa ba za su bukaci gwamnati ta biya kudin fansar yaran kuma za su iya sakin yaran a rukuni-rukuni.

“Suna kuma iya neman gwamnati ta saki manyan mayakansu da ke tsare a gidajen yari a fadin kasar nan.

“Yaran na da matukar amfani kamar ’yan matan Chibo. Bayan abun da ya faru a 2014 gwamnati ta yi ta amfani da hanyoyi daban-daban, ciki har da biyan kudin fansa da musayar tsararrun ’yan kungiyar da daliban”, inji shi.

 

Kar a yi amfani da karfi

Wani masanin harkar tsaro da wakilinmu ya zanta da shi ya ba da shawarar kar gwamnati ta yi amfani da karfi wurin ceto yaran.

“Za a shiga bala’i idan aka yi amfani da karfi wurin kwato yaran saboda Boko Haram na iya yin komai. Sai dai damar da gwamanti ke da shi a yanzu shi ne yankin da aka dauke daliban.

“Amma idan suka yi sanya wurin tattara bayanai, do ’yan ta’addar za su samu hanyar komawa Dajin Sambisa ko Dajin Alagarno a Jihar Yobe.

“Da zarar sun samu yin hakan to abu na gaba shi ne su sauya wa yaran tunani su zama mayaka, Allah Ya kyauta,” inji shi.

Parents wait to hear news about their abducted children outside the Government Science in Kankara, Katsina State yesterday, where gunmen abducted students of the school on Friday night.
Iyaye daliban na jiran labari game da ’ya’yansu sa aka yi garkuwa da su a GSS Kankara, Jihar Katsina.

Sojoji da Gwamnati sun yi gum

A daukacin ranar Talatar da kungiyar ta fitar da sakon ikirarin garkuwa da daliban, Gwamnatin Tarayya ko Fadar Shugaban Kasa ba ta ce uffan a kai ba.

Babban Mashawarcin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Garba Shehu bai amsa kiran waya da rubutaccen sakon da muka tura masa ba har muka kammala hada wannan rahoton.

Ita ma Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta yi gum da bakinta game da ikirarin da Shugaban Boko Haram ya yi.

Mun yi ta kiran Babban Jami’in Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar John Enenche domin mu ji ta bakinsa amma bai dauka ba, bai kuma amsa sakon da muka aika masa ta waya ba.

Ita ma Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, ba ta amsa bukatarmu ta samun bayani game inda aka kwana kan batun ba.

Mai magana da yawun Rundunar, Birgediya Sagir Musa bai amsa kiran wayar da muka yi maasa ba.

 

Soldiers comb the surroundings of the school yesterday
Sojoji na share wuraren da ke makwabtara da makarantar da aka sace daliban

 

‘Masari ya yi shiririta’

Wani tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Mike Ejiofor, ya shaida mana cewa bayanin da Gwamna Aminu Masari ya yi cewa gwamnati na tattaunawa da masu garkuwar ba ta da amfani.

Ejiofor ya ce: “Ban ga dalilin da gwamnati za ta fito ta cewa tana tattaunawa da ’yan bindigar ba”.

Tsohon shugaban na DSS ya ce babu bambanci tsakanin Boko Haram da ’yan bindiga tunda kowannensu manyan laifuka yake aikatawa.

“Ikirarin na nufin da karfinsu kuma sun bazu a sassan kasar na. Tunda har suka iya zuwa Arewa ta Yamma suka yi garkuwa da adadin mutanen da ba su iya yi ba a Arewa  maso Gabsa, to muna bukatar mu tashi wurjanjan”, inji Ejiofor.

 

A daina biyan kudin fansa

A nasa bangaren, mai sharhi kan ayyukan ta’addanci da kuma tara bayanan sirri na kasa da kasa, Dokta Amaechi Nwaokolo, ya yi kira da a daina biyan ’yan ta’adda kudaden fansa.

A cewarsa hakan na nufin tamkar gwamnatin kasar na tallafa wa ’yan ta’adda da kudade ne.

“’Yan bindigar na da alaka da Boko Haram. An gano cewa ’yan ta’adda na hada kai su yi aiki da gungun masu aika manyan laifuka; saboda haka tamkar ana ba wa masu laifi kudade ne” kamar yadda ya bayyana.

 

Babu gaskiya a bayanan masari

Wani Masani a kan harkar tsaro, Malam Kabir Adamu Matazu, ya ce babu kamshin gaskiya a maganar da Gwamna Masari ya yi cewa sun fara tuttaunawa da ’yan bindigar da suka sace daliban.

Idan ba a manta ba Masari ya shaida wa Shugaba Buhari cewa ’yan bindigar da suka dauke yaran sun tuntube su kuma an fara tattaunawa da su don su sako daliban.

Sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar bayan gawanar gwamnan ta Buhari ta ambato Masari na cewa an gano inda aka kai yaran kuma sojoji sun yi wa wurin kawanya.

“Abun takaici, sai ga Shekau ya fito ya fita yana cewa su ne suka dauke daliban.

“Wannan ya nuna yadda gwamnati ke rufa-rufa da abubuwa, sun yi waccan maganar ce domin su kwantar wa iyayen daliban hankali”, inji masanin”, inji shi.

 

Martanin ’yan Najeriya kan ikirarin Boko Haram

Malam Abubakar Lawan, daya daga cikin iyayen daliban da aka yi garkuwa da su ya ce kurarin na Shekau ba ta girgiza shi ba.

Abubakar daga Zariya ya ce ’ya’yansa uku ne suka bace bayan harin, amma daga baya daya daga cikinsu ya bayyana.

“Na ji a labaru Boko Haram na cewa ita ce ta dauke su amma ni ban dauki wannan a matsayin komai ba”, inji mahaifin daliban.

Ya ce tsoron da ake yi cewa kungiyar za ta sauya wa yaran tunani su zama ’yan ta’adda ba komai ba ne face rashin tawakkali.

“Insha Allah hakan ba zai taba faruwa da ’ya’yanmu ba, muna da kyakkyawan fata cewa za su dawo mana cikin aminci”.

Shi ma wani mahiafi da dansa ya bace, Malam Ibrahim Sulaiman, ya ce: “Ba yanzu masu garkuwa da mutane suka fara daukar mutane suna kaiwa daji don neman kudin fansa ba.

“Damuwata ita ce kwana biyu da sallamo dana daga asibiti kuma mun ji cewa ba su da abinci don an ga masu garkuwar na cin danyar taliyar yara da dalibai suka kai makaranta a sa’ilin da suka sace yaran”, inji shi.

A woman whose son was abducted sobs inside the school’s premises
Wata mata da aka yi garkuwa da danta cikin damuwa a harabar makarantar.

Amma wani mazaunin Kankara, Muhammad Shema ya bayyana damuwa game da ikirarin Shekau, yana mai cewa salon halin Boko Haram na kamanceceniya da na ’yan bindiga.

“Irin makamansu, yanayin rayuwarsu, cimarsu, yadda suke satar dabbobi, suke kai wa kauyuka hari suna fashin abinci da sauran abubuwan bukatun yau da kullum na kama sosai

“Wasu ma na tunanin kungiya daya ce take amfani da sunaye daban-daban saboda bambancin wuri, amma ba mu da karfin tabbatar da wannan ikirari. Muna bukatar a yi duk mai yiwuwa wurin tabbatar da sahihancinsa”, inji shi.

 

Ilimi na fuskantar barazana a Arewa —Anmesty 

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta yi tir da inda ta ce ya nuna harkar ilimi na cikin barazana a Arewacin Najeriya.

“Mun yi tir da harin wanda daya ne daga miyagun ayyukan Boko Haram. Tun  2012 kungiyar ke kashewa da jikkata daruruwan dalibai da malamai baya ga dubban daliban da ta yi gurkuwa da su.

“Kai wa makaratun hari da yin garkuwa da yara laifukan yaki ne; ya kamata a hukunta Boko Haram kan ikirarin ta na kai wa makarantu hari da sauran tauye hakkin dan Adam.

“Yaran da aka sace na cikin babban hadarin ana iya cutar da su ko tursasa musu daukar makami. Wajibin ne Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan dawo da su da ma sauran yaran da ke hannun kungiyar.

“Ilimi na cikin hari a Arewacin Najeriya alhali kamata ya yi makarantu su kasance wurare masu aminci; bai kamata a ce zabin da yaro ke da shi shi ne tsakanin ilimi ko rayuwarsa ba”, inji Amnesty.

 

A yi wa tufkar hanci —Majalisa

Ita ma Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamntin Tarayya ta magance barazanar da cibiyoyin ilimi ke fuskanta da a ’yan ta’adda a Arewacin Najeriya.

Majalisar ta bayyana hakan ne bayan kudirin da Honorabul Musa Sarkin Adar ya gabatar a zamanta na ranar Talara.

’Yan Majalisar sun nuna damuwa cewa an sha zuwa makarantu, ba a yankin Arewa ba kadai, ana yin garkuwa da dalibai.

A watan Afrilun 2014, Boko Harma ta kai hari a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata da ke Chibok, Jihar Borno inda da sace dalibai 276.

Ta kuma kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) a Buni Yadi, Jihar Yobe, ta yi wa dalibai kisan gilla ta kona ajujuwan makarantar.

“A watan Fabrairun 2018 an yi garkuwa da ’yan mata masu shekara 11 zuwa 19 Makarantar Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Dapchi, Jihar Yobe.

“An kai irin harin a Makarantar Karamar Sakandare ta Babington a Ikorodu, Jihar Legas, Sakandaren Turkish International, Isheri Jihar Ogun, Lagos State Senior Model College, lgbonia a Jihar Legas da Makarantar Sakandaren ’Yan Mata da ke Moriki a Jihar Zamfara,” inji dan Majalisar.

Majalisar ta yi kira ga Gwamantin Tarayya da ta gaggauta kawo karshen har-haren a kan makarantu a fadin Najeriya.

 

Mutuncin Najeriya ya zube —ACF

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta nuna takaicinsa game da yanayin tsaron Najeriya, wanda ta ce yana zubar da kimar kasar a idon duniya.

ACF ta ce da alama Gwamnatin Tarayya ba ta daukar matakan hana aukuwar irin wadanann munanan abubuwa.

Sakataren Yada Labaran Kungiyar, Emmanuel Yawe, ya yi bayanin ne bayan taron Kwamitin Amintattun Kungiyar.

“Tun a zamanta na watan Oktoba, ACF ta koka kan rashin tsaro amma ba abin da aka yi, yanzu ma a Disamba maganar muke yi, har yanzu ba a yi komai ba; har mun gaji da yin korafi.

“Gwamnati ta tausaya wa talakawa saboda suna cikin mawuyacin hali”, inji shi.

 

Ya kamata a zurfafa aikin tsaro

Jam’iyyar (APC) mai mulki, a nata bangaren ta bukaci hukumomin tsaro su fadada su kuma “zurafara” aikinsu wurin magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Gwamnan Yobe, kuma Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar na Kasa, Mai Mala Buni ya yi kiran a cikin wata sanarwa.

Buni ya bayyana kaduwarsa tare da tausaya wa iyalan daliban da abin ya shafa da ma gwamnati da jama’ar Jihar Katsina.