✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom din ISWAP ya kashe ’yan kasuwa 10, ya jikkata 20 a Borno

Ana zargin ISWAP ta dasa bom din ne ga sojojin da ke sintiri a yankin

Wata motar ’yan kasuwa ta tarwatse, inda fasinjoji 10 suka mutu, wasu 20 suka jikkata bayan da motar ta taka wani bom da ake kyautata zaton  ’yan ta’addan ISWSP ne suka dasa a Jihar Borno.

Wannan lamari ya faru ne a yayin da ’yan kasuwar ke tafiya a cikin mota a hanyar Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa ta jihar.

Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ’yan tada kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa motar ta fashe ne bayan ta kutsa kai cikin wata na’urar da ake kyautata zaton na dauke ne da wani bom da ke gefen hanya a ranar Laraba.

Rahoton na karin haske da cewar, an yi imanin cewa an ajiye bam din ne ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai, da ke sintiri a kusa da sansanonin ’yan kungiyar ta ISWAP.

Tunin dai aka kai wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Monguno inda suke karbar magani.