✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bomai na APC ya ci zaben Sanatan Yobe ta Kudu

Dan takarar Jam'iyar APC Ibrahim Mohammed Bomai ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Kudu

Dan takarar Jam’iyar APC, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Kudu.

Baturen zaben, Dokta Abacha Beleni ya bayyana cewa Bomai ya lashe zaben ne da kuri’u 69,596 sai wanda ya zo na biyu, Halilu Mazangane na Jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u  68,885.

Ya sanar da haka ne bayan tattara sakamakon zaben da aka karasa a ranar Asabar.

Sauran ’yan takarar su ne Yerima Adamu na ADC – 652; Jauro Ishaku na LP – 471; Isa Musa na NNPP – 3,277; sai Maisambo Barde na YPP – 448.

Da farko INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, bayan soke zaben wata rumfar zabe daya a Karamar Hukumar Fika.

Rumfar da aka soke zaben na da masu rajistar zabe 1,118 alhali a lokacin tazarar kuri’un 617 ne tsakanin ’yan takarar APC da PDP.