Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

Tare da

Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

227. An karbo daga Asim dan Aliyu ya ce: “Dan Abu Zi’ib ya ba mu labari daga Sa’idul Makburi daga babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Yin hamma daga Shaidan ne, idan dayanku ya yi hamma, to lallai ya rufe bakinsa gwargwadon ikonsa. Saboda lallai dayanku idan ya bude baki ya ce: Ha! Sai Shaidan ya yi masa dariya.”

228. An karbo daga Zakariya dan Yahya ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Lokacin da Yakin Uhudu ya kasance an karya mushirikai sai Iblis ya yi kuwwa (ihu) yana cewa: “Bayin Allah ku tafi ta karshenku!” Sai daya jama’a ta juyo ta yi karo da tafarko. Ana nan haka Huzaifa ya hango babansa Yaman yana tahowa sai ya rika cewa: “Bayin Allah Babana ne! Babana ne! Wallahi ba su hanu ba face sai da suka kashe shi (da rashin sani). Sai Huzaifa ya ce: “Allah Ya gafarta muku.” Urwa ya ce: “Huzaifa bai gushe ba cikin alheri (tunda ya nemi gafara ga wadanda suka kashe mahaifinsa) har sai da ya hadu da Allah.”

229. An karbo daga Alhasan dan Rabi’u ya ce: “Abul Ahwas ya ba mu labari daga Ash’as daga Babansa daga Masruk ya ce, A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Na tambayi Annabi (SAW) game da waiwayen mutum a cikin Sallah. Sai ya ce: “Wannan rikitarwa ce daga Shaidan wanda ke amfani da shi domin ya rikitar da dayanku.”

230. An karbo daga Abul Mughira ya ce: “Auza’iyyu ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba ni labari daga Abdullahi dan Abu Kattada daga Babansa daga Annabi (SAW).

231. An karbo daga Sulaiman dan Abdurrahman ya ce: “Walid ya ba mu labari ya ce, Auza’iyyu ya ba mu labari ya ce, Yahya dan Abu Kasir ya ba ni labari ya ce, Abdullahi dan Abu Kattada ya ba ni labari daga Babansa ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafarkin kwarai daga Allah yake. Amma yaye-yayen mafarki (sururun mafarki) daga Shaidan ne. Idan dayanku ya yi mafarki wanda yake jin tsoronsa, to lallai ya yi tofi ta gefen hagunansa kuma ya nemi tsarin Allah wannan mafarki ba ya cutar da shi.”

232. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Summiyu bawan Abubakar daga Abu Salih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya ce: “La’ilaha illahu wahdahu lasharika lahu, lahul mulk walahul hamdu wahuwa ala kulli shai’in kadir, (Babu abin bauta da gaskiya sai Allah ba Ya da abokin tarayya. Mulki naSa ne godiya taSa ce kuma Shi a kan dukkan komai Mai iko ne). Idan ya fadi haka sau dari a cikin yini tana daidai da ’yanta bayi dari. Kuma za a rubuta masa kyawawa dari, a shafe masa munana dari. Kuma za ta kasance masa kariya daga Shaidan a cikin yininsa wannan har sai ya yini. Kuma babu wanda ya kai shi aikin alheri face wanda ya aikata fiye da abin da  ya aikata.”

233. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari daga Salih daga Dan Shihab ya ce: Abdurrahman dan Abdurrahman dan Zaid ya ba ni labari cewa: Muhammad dan Sa’ad dan Abu Wakkas ya ba shi labari, cewa: lallai Babansa Sa’ad dan Abu Wakkas ya ce: “Umar ya taba neman izinin Manzon Allah (SAW) lokacin da yake tare da wadansu matan Kuraishawa suna yi masa magana kuma suna yawaita daga muryarsu sama da tasa (Annabi). Lokacin da ya yi wa Umar izini sai suka mike suna gaggawar neman hijabi. Sai Manzon Allah (SAW) ya yi masa izini lokacin Manzon Allah (SAW) yana dariyar matan nan. Sai Umar ya ce: “Me ya sa ka dariya ya Manzon Allah! Sai ya ce: “Ina mamakin wadannan mata ne. Wadanda ke tare da ni yanzu lokacin da suka ji muryarka sai suka rika gaggawar neman hijabi.” Sai Umar ya ce: “Kai ka fi cancanta su ji kwarjininka ya Manzon Allah a kaina!” Sa’an nan (Umar) ya fuskance su ya ce: “Ya ku makiya rayukansu! Shin kuna jin kwarjinina (tsorona) amma ba ku jin kwarjinin Manzon Allah (SAW)? Sai suka ce, “Na’am, kai ka fi ban tsoro kuma ka fi Manzon Allah (SAW) kaurin fushi.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunSa. Shaidan ba zai taba haduwa da kai bisa kowace hanyar da ka kama bin ta ba face ya sake ta, ya bi wata hanya.” (wannan hadisi mai yiwuwa ya faru ne kafin saukar ayar da ta hana daukaka murya sama da ta Manzon Allah (SAW) ne).