✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya amince a kashe N8.3bn don saya wa ’yan sanda motocin aiki

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan takwas da miliyan 300 don sayo motoci da sauran kayan aiki ga Rundunar ‘Yan Sandan…

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan takwas da miliyan 300 don sayo motoci da sauran kayan aiki ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Alhaji Mohammed Dingyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ta jagoranta a Fadar Shugaban Kasa a ranar Laraba.

Dingyadi ya ce kudaden da aka amince a kashe sun hada har da na samar da magunguna da sauran kayan kula da lafiya don amfanin asibitin ’yan sanda.

Ya ce, “A yau, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince wa Asusun Kula da Harkokin ’Yan Sanda (NPTF) ya ba da kwangilar sayo motocin aiki kirar Toyota guda 82 a kan kudi Naira biliyan 2.2 domin karfafa wa ’yan sandan Najeriya gwiwa wajen aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.

“Haka nan, mun amince a sayo rigar ruwa a kan kudi biliyan N1.9. da takalmin ruwa na miliyan N576, da kayan ba da agajin gaggawa ga marasa lafiya a kan biliyan daya, da kayayyakin koyarwa don amfanin makarantun ’yan sanda kan kudi miliyan N664.

“Za kuma a sayo magunguna da sauran kayan asibiti a kan biliyan biyu; yayin da aka hada wannan lissafin baki daya, zai kama jimillar biliyan 8.3,” inji shi.

Ministan ya ce bayan sayo duka wadannan kayayyakin, za a rabar da su ne yadda ya dace ga hukumomin ’yan sanda da ke sassan kasar daban-daban.

Ya kara da cewa an kafa NPTF musamman don bunkasa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta hanyar wadata ta da kayan aiki, ba da horo da kuma kula da walwar jami’anta.