✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya girgiza da rasuwar mahaifiyar Sarkin Kano

Buhari ya jajanta wa Masarautar Kano da Bichi da kuma Ilorin, mahaifar marigayiyar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero, mahaifiyar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

Buhari ya mika ta’aziyyarsa ne ga Masarautar Kano da Bichi da kuma Ilorin, mahaifar marigayiyar.

“Na girgiza da rasuwarta, kasancewarta uwa mai ba da kwarin gwiwa ga iyalanta da daukacin mutanen da ta hadu da su,” inji sakon ta’aziyyar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar.

“Hajiya Maryam Ado Bayero karimiya ce kamar mijinta, Sarkin Kano marigayi Ado Bayero.

“Ina jajanta wa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero; da Gidan Sarautar Ilorin, musamman Mai Martaba Sarki, Dokta Ibrahim Sulu Gambari da Shugaban Ma’aikatana, Farfesa Ibrahim Gambari.”