✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya halarci bikin naɗa sabon Sardaunan Dutse Nasiru Danu

Danu ta shiga harkar siyasa a 2002 a lokacin da Buhari ke shirye-shiryen tunkarar Zaɓen 2003.

Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya halarci bikin naɗin sabon Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru Haladu Danu

Tsohon shugaban ƙasar wanda ya kasance babban bako na musamman na ɗaya daga cikin tawagar manyan baƙi da ta haɗa da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar da suka halarci bikin naɗin a Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa.

Aminiya ta ruwaito cewa, naɗin Nasiru Danu a matsayin Sardaunan Dutse na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Dokta Maitama Bello.

Kafin naɗin na yanzu, Alhaji Danu shi ne mai riƙe rawanin Dan Amanar Dutse wanda tsohon Sarkin Dutse, Marigayi Nuhu Muhammad Sanusi ya naɗa masa a ranar 4 ga watan Mayun 2017.

Bayanai sun ce Alhaji Danu gogaggen ɗan siyasa kuma fitaccen ɗan kasuwa da ke riƙe da jagorancin Kamfanin Casiva Limited wanda ya assasa Gidauniyar Nasiru Danu.

Sabon Sardaunan Dutsen ya jefa ƙafarsa cikin harkokin siyasa a shekarar 2002 lokacin da aka soma tafiyar goyon bayan Buhari a shirye-shiryen tunkarar Zaɓen 2003.

Ga wasu hotunan manyan baƙi da suka halarci bikin naɗa sabon Sardaunan Dutsen