Bayan wata 7, Buhari ya sake bude Twitter a Najeriya | Aminiya

Bayan wata 7, Buhari ya sake bude Twitter a Najeriya

    Sagir Kano Saleh

Al’ummar Najeriya sun ci gaba da amfani da kafar sadar da zumunta ta Twitter, bayan gwamnatin kasar a janye dakatarwar da ya yi wa harkokin kamfanin Twitter a kasarta.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya janye takunkumin da ya sanya wa harkokin Twitter a kasar ne bayan kamfanin ya shafe watanni yana neman sasanci, tun bayan da gwamnatin Najeriay ta rufe harkokinsa a kasar.

“Shugaba Buhari ya amince dage dakatarwar ta fara aiki daga karfe 12 na dare, ranar 13 ga watan Janairu, 2022” inji sanarwar da gwamnatin ta fitar.

Shugaban Kwamitin Aiki da Cikawa Kan Tattaunawar Gwamnatin Najeriya da Kamfanin Twitter, kuma Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Harkokin Sadarwar Zamani ta Najeriya (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, shi ne ya sanar da hakan.

Kashifu ya ce an janye takunkumin Twitter ne bayan wasikar da Shugaba Buhari ya aike wa Ministan Sadarwar Zamani, Isa Ali Ibrahim.

A watan Yunin 2021 ne Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da harkokin Twitter a kasar, bayan kamfanin ya goge wani sako da Shugaba Buhari ya wallafa shafinsa na Twitter ka ayyukan ta’addancin haramtacciyar kungiyar IPOB.

A sakamakon haka ne Gwamnatin Najeriya ta zargin kamfanin da yi mata zagon kasa da kuma bayar da kafarta ga masu neman raba kan ’yan Najeriya da tayar da fitina a kasar domin tayar da zaune tsaye.

Tun daga lokacin al’ummar Najeriya suka daina amfani da Twitter, sai dai ta bayan fage.

Bayan haka ne kamfanin ya nemi sasanci da gwamantin, inda ita kuma ta gindaya masa sharudda da sai ya cika kafin ta amince ya ci gaba da gudanar da harkokinsa a kasar.

A kan haka ne gwamantin ta kafa kwamiti na musamman kan lamarin, daga bisa na kafa kwamitin aiki da cikawa da zai yi aiki kai tsaye da bangaren kamfanin domin ganin bai yi wa kasar manakisa ba.

Sharuddan sun hada da biyan haraji ga gwamnatin da kuma bude Ofishin Twitter a Najeriya inda kuma jami’in kamfanin a Najeriya zai rika gudanar da aikinsa.

Tun a wancan lokacin ne gwamnatin ta kafa kwamitin tattauna daga bangarenta da na kamfanin, wanda ya amince da sharuddan da aka gindaya masa, kuma zai cika.

A lokacin, kamfanin ya bayar da uzurin cewa ba zai iya cika sharadin bude ofishinsa a Najeriya ba sai zuwa farkon shekarar 2022 da muka shiga.

Tun a bara, Minsitan Sadarwa, Lai Mohammed, ya sanar cewa ana dab da bude Twitter a Najeiyra.