✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da shirin bunkasa rayuwa zuwa 2050

A shekara 30 Shirin muradun kasa na Agenda 2050 zai azurta mutum miliyan 100

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin shirin muradun bunkasa Najeriya cikin shekara 30 mai suna Agenda 2050.

Agenda 2050 mai muradin kyautata rayuwar ‘yan Najeriya cikin shekara 30 masu zuwa, zai gaji shirin Vision 2020 na gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa ‘YarAdua ta kaddamar a 2009 da kuma shirin ERGP da aka kafa a 2017 domin habbaka da tattalin arzikin kasar.

Ana hasashen Agenda 2050 zai fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci daga yanzu zuwa 2050, la’akari da hasashen Bankin Duniya ke cewa yawan ‘yan Najeriya zai kai miliya 400 zuwa shekarar 2040.

Buhari ya kaddamar da kwamitin ne karkashin jagorancin hamshakin dan kasuwa Atedo Peterside da kuma da kuma Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmed.

Kwamitin zai kunshi wakilcin gwamna daya daga kowacce daga shiyyoyin siyasa shida na kasar; sai kuma wakilcin ‘Yan Majalisa Wakilai da na Dattawa da Ministoci da hukumomi da manyan jam’iyyu da ‘yan kasuwa da ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki.