✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kadu da hatsarin jirgin ruwan Bagwai

Buhari ya nuna damuwarsa matuka kan faruwar hatsarin jirgin ruwan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana damuwarsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya afku a ranar Talata a Karamar Hukumar Bagwai da ke Jihar Kano.

Hatsarin kwale-kwalen wanda ya yi ajalin sama da daliba 20 na wata makarantar Islamiyya ya kada Shugaba Buhari, inda ya bayyana lamarin a matsayin iftilai mai ta da hankali.

Cikin sanarwar da Buhari ya fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Garba Shehu, ya ce gwamnatin tarayya za ta tallafa wa mahukunta a fagen aikin ceto wanda hatsarin ya rutsa da su.

Kazalika, shugaba Buhari ya jajanta wa al’ummar Jihar Kano kan faruwar lamarin, inda ya yi gargadin da a kiyaye faruwar hakan a gaba.

“A yayin da ake ci gaba da ceto mutanen da hatsarin ya rutsa da su, ina addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu tare da fatan samun nasarar ceto ragowar,” a cewar sanarwar.

Hatsarin jirgin ruwa na baya-bayan rahotanni sun ce fiye da mutum 30 ne ake tunanin sun bata bayan hatsarin kwale-kwalen.

Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce kwale-kwalen yana dauke ne da mutum kusan 50.