✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya mika wa Majalisa kudurin sabuwar dokar kudaden sata

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa Majalisar Wakilai kudurin dokar Yaki da Ta’addanci da kuma ta Hana Ta’ammali da Haramtattun Kudade domin amincewarta.  Da…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa Majalisar Wakilai kudurin dokar Yaki da Ta’addanci da kuma ta Hana Ta’ammali da Haramtattun Kudade domin amincewarta. 

Da yake karanta wasikar Buhari a zauren Majalisar a ranar Alhamis, Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Idris-Wase, ya bayyana cewa kudurin zai magance gibin da ake da ita a Dokar Yaki da Ta’addanci da Haramtattun Kudade, domin ta dace da ta sauran kasashen duniya.

Buhari transmits money laundering, terrorism prevention bills to Reps

Wasikar ta Buhari ta ce, “A taron nazarin kungiyoyi kan yaki da safarar haramtattun kudade a Yammacin Afirka, akwai wasu gibi da aka gano a tattare da dokar Najeriya kan yanki da safarar haramtattun kudade da kuma yaki da ta’addanci ta Najeriya.

“Bayan nazarin ne Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya tare da sauran masu ruwa da tsaki suka yi wa dokokin gyran fuska.

“Dole sai an gyara wannan tawayar daga Majalisar Dokoki ta Kasa domin dokokin su dace da shawarwarin Kwamitin Aiki da Cikawa Kan Kudade na Majalisar Dinkin Duniya, idan ba haka ba Najeriya na iya fuskantar matsala ciki har da takunkumi daga kwamitin, wanda hakan zai yi illa ga tattalin arzikinmu.

“Saboda haka ma’aiktar ta sake nazari tare da yi wa kururin dokokin gyaran ta kuma gabatar wa majalisa domin a sumu sabbin dokokin, lura da wadancan abubuwa da ka ambata.”