✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada wa hukumar kula da gidajen gyaran hali da ta NSCDC sabbin shugabanni

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tsaro ta NSCDC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tsaro ta NSCDC biyo bayan ritayar tsohon shugabanta, Abdullahi Gana Muhammad.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Mohammed Manga ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Ahmed ya sami nasarar darewa kujerar ne bayan da ya sami kaso mafi tsoka a sakamakon tantancewar da ma’aikatar ta yi wa masu zawarcin kujerar, a wani mataki na tabbatar da wanda ya fi cancanta ne aka ba shugabancin hukumar.

Kazalika, Shugaba Buhari ya amince da nadin Halliru Nabani a matsayin sabon Kwanturolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS).

Duka nade-naden za su fara aiki ne da zarar Majalisar Dattawa ta amince da su.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya taya sabbin shugabannin hukumomin murnar nadin tare da kiransu da su jajirce wajen ba mara da kunya.

Abdullahi Gana Muhammad dai ya yi ritaya ne sakamakon karewar wa’adinsa a ranar 17 ga watan Janairun 2021.

Idan za a iya tunawa, sai da Minista Aregbesola ya kara wa Gana watanni shida a kan wa’adinsa a watan Yulin 2020.

Daga nan ne kuma aka nada Mataimakin Kwamandan hukumar mai kula da Ayyuka na Musamman, Kelechi Hilary a matsayin mai rikon mukamin shugaban hukumar ta NSCDC.