✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nemi gafarar iyayen daliban da aka sace —PDP

Jam'iyyar PDP ta ce tabbas shugaba Buhari ba shi da wata nagarta da zai iya jan ragamar shugabancin Najeriya.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci Shugaba Buhari ya nemi gafarar iyayen daliban GSSS Kankara da aka sace a Jihar Katsina saboda hayaki mai sanya hawaye da jami’an tsaro suka harba musu a yayin da suka zanga-zanga ranar Lahadi.

Mazauna sun ce iyayen yaran da aka sace sun fito kan titunan Katsina a ranar Lahadi, don nuna bacin ransu game da sace daruruwan daliban makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankara a ranar Juma’a.

“Abun takaici, maimakon a bi sahun ’yan bindigar da suka sace yaran sai aka bige da amfani da karfin iko ana azabtar da marasa karfi.

“Irin wannan halin ko in kula da Gwamnatin Buhari ke nunawa ya bayyana a fili jami’iyyar cewa APC ta gaza matuka. A kwanakin baya haka ’yan ta’adda suka yi wa manoma 43 kisan killa.

“Jam’iyyarmu tana taya iyayen wadannan yara da aka sace alhini; duk da cewa Shugaba Buhari ya je Katsina yin hutu amma hakan bai amfanar da komai ba.

“Don haka PDP na kira ga Fadar Shugaban Kasa ta umarci Buhari da ya nemi  gafarar ’yan Najeriya da iyayen daliban da aka sace tare da daukar matakan ladabtar da wadanda suka ba da umarnin amfani da barkono tsohuwa a kan iyayen yaran.

“Muna kira ga Buhari da ya hanzarta ba da umarnin yin amfani da duk kayan aikin da ake da su a jihar domin kubutar da yaran baki daya.

“PDP tare da hadin gwiwar ’yan kishin kasa da mutanen Katsina ba za mu daina kira ba har sai Buhari ya kubutar da wadannan yara da aka sace baki daya”, inji sanarwar da kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Lahadi.

Jam’iyyar ta ce tabbas shugaba Buhari ba shi da wata nagarta da zai iya jan ragamar shugabancin Najeriya duba da yadda abubuwa ke ci gaba da tabarbarewa karkashin ikonsa.