✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa Kasar Kuwait ta’aziyya kan rasuwar Sarkinta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah. Sakon ta’aziyyar Shugaban Kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.

Sakon ta’aziyyar Shugaban Kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya janjanta wa Gwamnati da daukacin al’ummar kasar Kuwait dangane da rasuwar Sarkin wanda ajali ya katse masa a ranar Talata.

Buhari ya jinjina wa Marigayin Sarkin wanda a cewarsa ya jijirce wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin Kasashen da ke yankin Gulf a tsawon shekaru 14 a ya shafe a karagar mulki.

Kazalika shugaban kasar ya taya sabon sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, murna wanda aka nada kwana daya bayan mutuwar yayansa.

Buhari ya nemi Sheikh Nawaf da ya yi koyi da kyawawan tsare-tsare da akidu irin na dan uwansa wajen kara wa dangartakar da ke tsakanin Najeriya da Kuwait karfi.