✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Saudiyya don yin Umararsa ta karshe a matsayin Shugaban Kasa

Wannan ce za ta kasance Umararsa ta karshe a matsayin Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata zai tafi kasar Saudiyya don gudanar da ibadarsa ta Umarah ta karshe a matsayin Shugaban Najeriya.

Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan ranar Litinin, inda ya ce ziyarar zai yi ta ne daga ranar 11 zuwa 19 ga watan Afrilun 2023.

Sanarwar ta kuma ce ko a ranar Juma’a sai da Buharin ya halarci bikin rufe Tafsirin Alkur’ani mai girma na watan Ramadan a masallacin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, a shirye-shiryen limamin masallacin na tafiya Saudiyya don yin Umara.

Garba Shehu ya ce duk da kasancewar a kowacce shekara ake gudanar da Tafsirin, amma Shugaba Buhari ya dauki na bana da matukar muhimmanci kasancewarsa na karshe kafin barinsa wa’adin mulki.

Ya kuma ce yayin rufe tafsirin, Babban Limamin masallacin ya yaba wa Buhari kan yadda ya ce ya dabbaka gaskiya da rikon amana da adalcin da tarihi ba zai manta da shi ba, a zamanin mulkinsa.

Ya kuma ce an yi addu’o’i na musamman don ganin an mika mulki cikin ruwan sanyi ga zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.