✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai rufe asusun bankin da ba su da BVN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa zawi rufe asusun bankin duk wadnada ba su da lambar BVN ko ta NIN.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa zawi rufe asusun bankin duk wadnada ba su da lambar BVN ko NIN. 

CBN ya cewa daga watan Afrilun 2024, duk asusun bankin da ba a hada da lambar BVN ko NIN ba, za su daina aiki.

Babban bankin ya umarci duk masu asusun banki da na e-wallet da su tabbata sun hada su da NIN ko BVN dinsu kafin 31 ga watan Janairu, 2024.

Sanarwar da CBN ya fitar dauke da sa hannun daraktan kudade da na tsare-tsare, Chibuzo Efobi da Haruna Mustapha, ta ce daga watan Afrilun 2024, “za a haramta sanya kudi ko cirewa aga asusun banki marasa BVN ko NIN.”

BVN shi ne lambar tantance masu ajiyar banki wanda CBN ya bullo da shi, wanda kowane mutum aka hade duk asusunsa na banki da BVN daya.

NIN kuma ita ce lambar shaidar dan kasa, wanda a watannin baya Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa kowa hade nasa da lambobin wayarsa.